Kutu Zata Hukunta Maryam Yahaya, Kan Yaron Da Ya Sha Fiya Fiya

0

WANI mutum, Muhammad Lawal Gusau, wanda mai rajin kare haƙƙin ɗan’adam ne, ya maka fitacciyar jarumar Kannywood, Maryam Yahya, a Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna bisa zargin ta da nuna halin ko-in-kula a kan wani matashi da ya sha guba saboda ita.

Shi dai matashin, mai suna Muhammad Gashua, ya je Kano ne daga Yobe don ya gana da gwanar tasa, amma rashin samun ganin nata ya sa ya nemi ya kashe kan sa.

Kwanan nan, an ga wani bidiyo a soshiyal midiya mai nuno wasu mutane zagaye da wani matashi su na ta ƙoƙarin ceto ran sa bayan ya kwankwaɗi maganin ƙwarin nan mai suna fiya-fiya.

An ce matashin ya sha wahalar neman inda da zai ga Maryam Yahya ne amma haƙar sa ba ta cimma ruwa ba. 

Wata majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa tun da fari sai da ɗan Gashuwan ya je situdiyon mawaƙi Ado Gwanja, ya tambaye su inda zai gan ta, su kuma su ka ce masa ba ta nan. 

Daga nan ne sai labarin ya canza, domin kuwa can aka hango shi ya galabaita, ya na kakarin mutuwa. Nan da nan jama’a ta taru, aka sawo madara aka yi ta ɗura masa, sannan aka kai shi asibiti. Allah ya taimake shi, ya murmure bayan an yi masa magani.

A nata ɓangaren, Maryam ba ta fito ta ce uffan a kan al’amarin ba, wato kamar ta nuna wa duniya damuwar ta da halin da matashin ya shiga a dalilin ta duk da irin ce-ce-ku-cen da aka yi a soshiyal midiya.

Related Post:-

A yayin da ɗan Gashuwan ya yi ƙoƙarin kashe kan sa, sai aka ga hotunan ta a soshiyal midiya, ta shirya gagarumin bikin murnar zagayowar ranar haihuwar ta, inda ta yi shiga ta kece raini. Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su game da halin ko-in-kula da ta nuna a kan mai son ta ɗin nan Muhammad Gashua.

Hakan ne ya fusata Muhammad Lawal Gusau har ya maka ta a kotu a jiya Litinin, 27 ga Yuli, 2020 madadin Gashua.

Muhammad Gashua jim kaɗan bayan an ɗura masa madara don a ceto ran shi

Idan masu karatun mu ba su manta ba, shi dai Gusau shi ne wanda a cikin Fabrairu 2020 ya maka mawaƙi Ibrahim Ahmad Rufa’i (Deezell) a kotu bisa zargin cewa shi ne ya fitar da bidiyon tsiraicin Maryam Booth, abin da shi kuma ya musanta.

Sai dai kuma abin mamaki, kwana ɗaya da fitar takardar ƙarar da Gusau ɗin ya yi, a yau sai ga hoton Gashua da Maryam Yahya ya ɓulla a soshiyal midiya. Wannan ke nuni da cewa akwai alamar jarumar ta tsorata da ƙarar da aka shigar a kan ta.

Mujallar Fim ta yi ƙoƙarin jin ta bakin jarumar a kan wannan al’amari, amma abin ya ci tura domin ba a samun ta a waya.

MUHAMMAD LAWAL GUSAU NE YA YI ƘARAR MARYAM A MADAƊIN ƊAN GASHUWA.

Ga hoton Sa A Nam Sama Da Sunan Shi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Sharing is Awesome, Do It!

Share this post with your friends
close-link