Kuyi addu’ar Allah ya kawo Ƙarshen Ta’addanci a Najeriya idan kunje Makka — Matawalle ga Maniyyata Aikin Hajji

0

Kuyi addu’ar Allah ya kawo Ƙarshen Ta’addanci a Najeriya idan kunje Makka — Matawalle ga Maniyyata Aikin Hajji - Dimokuradiyya

Kuyi addu’ar Allah ya kawo Ƙarshen Ta’addanci a Najeriya idan kunje Makka — Matawalle ga Maniyyata Aikin Hajji

Gwamnan Jahar Zamfara Bello Mohammed Matawalle yayi kira ga Maniyyata Aikin Hajji na Jahar dasu yi addu’a tuƙuru akan Allah ya maido da zaman lafiya da lumana a dukkanin sassan Najeriya idan sunje Ƙasa mai tsarki.

Gwamnan yayi wannan kiran a lokacin da yake bankwana ga Maniyyata Aikin Hajji dubu 1,303 wanda zasu gudanar da aikin Hajjin wannan Shekarar a Ƙasar Saudiyya.


Download Mp3

Gwamna Bello Matawalle yace Jahar Zamfara na buƙatar Addu’o’i akan matsalar rashin tsaro dake damun ta.

Yace aikace-aikace ƴan bindiga a Jahar na bukatar roƙon ɗauki, sannan akwai buƙatar Maniyyata Aikin Hajji dasu yi addu’ar Allah ya maido da zaman lafiya a dukkanin sassan Jahar.

Gwamnan yayi kira a garesu dasu zama Jakadu na Ƙwarai na Jahar, gami da mutunta Dokokin Najeriya da kuma Ƙasar Saudiyya wadda itace mai masaukin su a Ƙasa mai tsarki.

Matawalle yace Gwamnatin sa ta bayar da dukkanin gudunmuwa daya shafi kuɗaɗe domin tallafawa Maniyyata Aikin Hajji domin su gudanar da ibadar su cikin sauƙi.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy