Kuyi hukunci mai tsanani ga duk wanda kuka samu da laifin Safarar mutane – Sakon NAPTIP ga Alkalai

0

Kuyi hukunci mai tsanani ga duk wanda kuka samu da laifin Safarar mutane – Sakon NAPTIP ga Alkalai - Dimokuradiyya

Dakta Fatima Waziri-Azi, babbar daraktar Hukumar Yaki da Fataucin Bil Adama ta Kasa (NAPTIP), ta yi kira ga alkalai da su yi hukunci mai tsanani ga duk wanda suka samu da laifin Safarar Bil’adama.

Dakta Fatima ta yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa a Abuja mai dauke da sa hannun Mista Vincent Adekoye, mataimakin jami’in hulda da jama’a na hukumar.

Ya bayyana cewa, Waziri-Azi ta yi wannan kiran ne a wajen bude taron yini biyu na karawa kungiyar alkalai mata ta kasa (NAWJN), tare da hadin gwiwar Cibiyar Shari’a ta kasa (NJI).


Download Mp3

Dakta Fatima ta yi kira ga Alkalai a fadin tarayya da su sanya irin wannan matakin na takunkumi kan shari’o’in cin zarafin mata.

Ta bayyana cewa masu laifin safarar mutane da masu laifin cin zarafin matan, ya kamata a yanke musu hukunci daidai da girman laifuffukan da suka aikata.

Ta yi nuni da cewa, a baya wasu daga cikin masu laifin kan je gida tare da yanke musu hukunci mai sauki, inda ta kara da cewa hukumar ta samu labarin wadanda suka sake aikata laifin kuma hakan na da matukar hadari ga al’umma.

A cewarta, Alkalai na da rawar da za su taka wajen kawar da fataucin mutane, da dakile cin zarafi da kuma rage laifukan cin zarafin mata.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy