Labarin Wasu Hassan Sa Hussaini Kumah Mawakan Asali, Da Suka Shahara:-

Fitattun Mawaƙan Nan Da Ake Kira Tagwayen Asali Sun Bayyana Cewa ‘yanbiyu Za Su Aura, Kuma Sun Bayyana Hoton ‘yanmatan.

Kwanan nan ne aka yaɗa wasu hotunan kafin aure da ake yi a wannan zamani (prewedding pictures) na mawaƙan biyu tare da wasu kyawawan ‘yanmata waɗanda su ka shiga iri ɗaya a soshiyal midiya.

Ganin hotunan ya sa aka riƙa yi wa tagwayen addu’o’in fatan alheri, a tunanin cewa aure za su yi.

Mujallar Fim ta bi bahasin hotunan ta hanyar tuntuɓar Hassan Abubakar Sani da Hussaini Abubakar Sani (Tagwayen Asali), inda su kuma su ka tabbatar mana da cewa babu shakka waɗannan ‘yanmatan ne za su aura.

A yayin da su ke yi mana ƙarin bayani, musamman ganin cewa babu wani takamaiman lokacin da aka sa za a yi bikin nasu, Tagwayen Asali sun faɗa wa mujallar Fim cewa, “Abin da ya faru, mun yi wannan hoton ne a wurin bikin murnar zagayowar ranar haihuwar ‘yanmatan (birthday). Shi ne aka ɗauki hoton ake yaɗawa a matsayin za mu yi aure. Amma dai su ‘yanmatan za mu aura, sai dai ba a saka rana ba. Wannan shi ne gaskiyar magana.”

To Allah ya nuna mana lokacin, Masoya Ku Tura Zuwa Facebook WhatsApp Twitter Instagram Da Sauran Social Media.

Kada Ku Manta Ku Kasance CE Tare Damu A Koda Yaushe Domin Samun Sabbin Labaran Kannywood Da Wakokin Siyasa Dana Hausa Duk A wannan Shafin.