Majalisar dokokin Kano ta amince da dokar siyawa Alkalai mota
Majalisar dokoki ta jihar Kano ta amince da dokar siyawa alkalan kotun Majistire dana Shari’a motoci duk bayan shekaru biyar.
Majalisar dokokin ta amince da yiwa wani bangare na dokar garambawul.
Majalisar karkashin shugabanta Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ta amince da dokar ne a zaman ta na jiya Talata.
Gyaran da aka yiwa bangaren shari’ar ya shafi Alkalan kotunan Majistire dana kotunan Shari’a da lauyoyi da kuma ma’aikatan shari’a.
Shugaban masu rinjaye na majalisa kuma dan majalisa mai wakiltar Warawa Labaran Abdul Madari, yace dokar ta kunshi siyawa alkalai motoci duk bayan shekaru biyar da basu alawus din naira dubu dari duk shekara.
Ya kara da cewa dokar zata bada damar duba lafiyar alkalan da sauran dokoki.
