Majalisar Dokokin Kano Ta Nada Sabon Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye

0

Majalisar Dokokin Kano Ta Nada Sabon Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye - Dimokuradiyya

A ranar Talata ne majalisar dokokin jihar Kano ta nada Magaji Zarewa a matsayin mataimakin shugaban masu rinjaye bayan murabus din Abdullahi Yaryasa.

Yaryasa ya yi murabus ne bayan ya fice daga jam’iyyar APC zuwa NNPP.

Shugaban majalisar, Hamisu Chidari, wanda ya karanta wasikar murabus din Yaryasa a zauren majalisar, ya yi masa fatan alheri a sabuwar jam’iyyarsa tare da gode masa bisa dimbin gudunmawar da ya bayar a majalisar.

Chidari ya kuma taya Zarewa mai wakiltar mazabar Rogo murnar nadin da aka yi masa tare da ba shi tabbacin goyon bayan majalisar.

Zarewa ya samu yabo a majalisar bisa zaboshi matsayin wanda ya cancanci sabon nadin.


Download Mp3

A wani labarin kuma Jam’iyyar APC ta kara yin asarar sanatoci 2 a hannun PDP

Jiga-jigai biyu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Yahaya Abdullahi; da Adamu Aliero, sun koma jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a hukumance, kamar yadda NAN ta ruwaito.

Ficewar Sanatocin APC guda biyu daga jihar Kebbi an mika su ne a wasiku daban-daban guda biyu zuwa ga shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, kuma aka karanta a zauren majalisar a ranar Talata.

Sanata Ailero da Sanata Abdullahi suna wakiltar mazabar Kebbi ta tsakiya da Kebbi ta Arewa.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Enyinnaya Abaribe, wanda ya sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyyar All Progressives Grand Alliance wato APGA a ranar 15 ga watan Yuni shekarar.

An dage sauya shekarsa da ficewarsa a matsayin shugaban marasa rinjaye, ganin yadda shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya kasa zuwa da wasikar sauya sheka da murabus dinsa daga mukamin zuwa zauren majalisa.

Duk da cewa Lawan ya sanar da hakan, amma an amince cewa an karanta wasikar Abaribe a kasa kafin ya fice daga matsayinsa na Shugaban marasa rinjaye, bayan wani batu da Sanata Gabriel Suswam (PDP daga Benue ya gabatar).

Haka kuma ya rage yawan Sanatocin APC daga 71 zuwa 69 a Majalisar Dattawa.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy