- Advertisement -

Makomar Ƙasar nan mai muni ce idan ba’a shawo kan matsalar Yajin Aikin ASUU ba — Malaman Kirista

0

Makomar Ƙasar nan mai muni ce idan ba’a shawo kan matsalar Yajin Aikin ASUU ba — Malaman Kirista - Dimokuradiyya

Makomar Ƙasar nan mai muni ce idan ba’a shawo kan matsalar Yajin Aikin ASUU ba — Malaman Kirista

- Advertisement -

Shuwagabannin Coci sun bayyana rashin jindaɗin su akan dogon yajin aiki da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ke cigaba da yi.

Sun bayyana cewar makomar ƙasar zata munana a yayinda Ɗalibai ke cigaba da yawo akan tituna babu abinda suke yi kullum.

Shuwagabannin sun yi jira ga Ƙungiyar ASUU da sauran Ƙungiyoyi dasu yi gaggawar sasanta dukkanin abubuwan da suke buƙata domin Ɗalibai da kuma makomar Ƙasar.

- Advertisement -

Shugaban Cocin Bible-believing churches ƙarƙashin jagorancin Fasto Abel Aiyedogbon a lokacin da yake jawabi ga Manema labaru a Ilori a ranar Litinin yace ƙasar zata munana idan har Matasa ba’a horas dasu kan gudunmawar da zasu bada ga Ƙasar.

Yace “a matsayin Ƙungiya da kuma sauran masu ruwa da tsaki, muna kira ga ɓangarorin guda biyu musamman Gwamnatin Tarayya data yi gaggawar shawo kan matsalar yajin aikin ASUU.

Ya bayyana cewar Ɗaliban da lamarin ya shafa sune Shuwagabannin gobe na Kasar, idan ya zaman to ba’a koya masu abinda zasu yiwa Ƙasar ba, makomar ƙasar zai ɓaci.

- Advertisement -

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy