Mun samu nasarori a yaƙi da Matsalar Tsaro, yanzu haka zaman lafiya ya dawo a wasu garuruwa — Buhari

0

Mun samu nasarori a yaƙi da Matsalar Tsaro, yanzu haka zaman lafiya ya dawo a wasu garuruwa — Buhari - Dimokuradiyya

Mun samu nasarori a yaƙi da Matsalar Tsaro, yanzu haka zaman lafiya ya dawo a wasu garuruwa — Buhari

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis a Kano yace Gwamnatin sa zata ɗauki tsatstsauran Mataki dake haifar da Tsoro da Matsalar Tsaron Najeriya.

Shugaban yayi kira ga Sabbi da Jami’ai na Rundunar Ƴan Sandan Najeriya dasu ƙara azama domin cigaba da tsaron Ƙasar akan ƴan ta’adda wanda suke so kullum ƴan ƙasa su kasance cikin tsoro.

Dayake jawabi a lokacin bikin yaye Ƴan Sanda na Makantar Horas da Ƴan Sanda ta Wudil Kano, Shugaba Buhari yace Gwamnatin sa nayin aiki tuƙuru da Tattalin Arzikin ta domin ganin ta sanya Rundunar Ƴan Sandan Najeriya “daga cikin jami’an tsaro Masu ƙarfi a faɗin Duniya.”

Babban Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa akan Kafafen Yaɗa Labaru Garba Shehu, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis mai taken “mun cimma nasarori ta fuskar tsaro, Tattalin Arziki, Cin Hanci, inji Shugaba Buhari, sai ya buƙaci ƴan sanda dasu aiki da Fasahar zamani’.

Dayake bada jawabi akan yaki da Matsalar Tsaro, Buhari yace Ƴan Boko Haram, da Ƴan IPOB, da Ƴan Bindiga a wasu sassan Ƙasar, an rage masu karfi sosai, kumi tuni zaman lafiya ya dawo a wasu garuruwa da ƙauye.

Yace wannan ƙoƙari dole za’a cigaba da yin sa domin ganin zaman lafiya ya dawo a ko’ina, musamman wuraren dake fama da matsalar ƴan bindiga.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy