- Advertisement -

Mun tura manyan jami’an yan sanda Jihar Osun Domin Zaben Dake Tafe—- Usman Alkali Baba

0

Mun tura manyan jami’an yan sanda Jihar Osun Domin Zaben Dake Tafe—- Usman Alkali Baba - Dimokuradiyya

Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba, ya tura manyan jami’an ‘yan sanda domin gudanar da zaben gwamnan jihar Osun da za a yi ranar 16 ga watan Yuli, inda ya yi alkawarin tsaurara matakan tsaro domin gudanar da zaben.

- Advertisement -

Ya kuma yiwa kwamishinan ‘yan sandan jihar Osun Olokode Taoheed Olawale kiranye zuwa hedikwatar rundunar na wucin gadi har zuwa lokacin da za’a kammala zabe sannan ya maye gurbinsa da, CP Julius Alawari daga helkwatar rundunar zuwa jihar

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya ce mataimakin sufeto-janar na ‘yan sanda mai kula da sashen binciken manyan laifuka na rundunar (FCID), DIG Johnson Babatunde Kokumo ne zai sa ido a zaben.

Wadanda za su taimakawa Kokumo sun hada da mataimakan sufeto-janar na ‘yan sanda hudu, da kwamishinonin ‘yan sanda hudu, da mataimakan kwamishinonin ‘yan sanda 15, da mataimakan kwamishinonin ‘yan sanda 30.

- Advertisement -

A cewar kakakin rundunar, an kuma tura isassun jami’an ‘yan sanda masu matsayi na manyan Sufetotin ‘yan sanda da kasa domin gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da limana.

Ya bayyana cewa, DIG Kokumo ne ke da alhakin sa ido kan aiwatar rundunar a jihar, don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ba tare da tashin hankali ba da kuma tabbatar da ‘yan kasa masu bin doka da oda a jihar susami walwalar gudanar da ayyukansu na al’umma ba tare da cin zarafi ko tsoratarwa ba .

Ya kuma yi bayanin cewa, sauran manyan jami’an da aka tura suna da alhakin daidaita ayyukan mutane da sauran ayyukan a gundumomin uku, kananan hukumomi 30 da kuma rumfunan zabe 3,753 a jihar Osun.

- Advertisement -

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy