Mutane 120 Ne Ke Kwance a Asibiti A Kano, Sakamakon Fashewar Iskar Gas Tare Da Gurbata Iska

0

Mutane 120 Ne Ke Kwance a Asibiti A Kano, Sakamakon Fashewar Iskar Gas Tare Da Gurbata Iska - Dimokuradiyya

Akalla mutane 120 ne aka kwantar da su a asibiti bayan da ake zargin wasu sinadarai masu guba daga wata iskar gas din masana’antu da ta kare sun gurbata iska tare da bazuwa unguwar Mundadu da ke wajen birnin Kano.

Mazauna yankin sun ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Juma’a inda wani Saifullahi ya tattaro tarkacen karafa ya murkushe su domin sake yin amfani da su.

Dagacin unguwar Magaji Abdullahi, yayin da yake magana kan lamarin ya ce, “Da yammacin yau ne aka sanar da ni cewa an samu matsala inda Saifullahi Muhammad yake sana’ar tattara karafa.”


Download Mp3

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kai da dama daga cikin wadanda suka jikkata zuwa asibitoci domin kula da lafiyarsu.

“Kusan 70 daga cikinsu an kai su cibiyar kula da lafiya matakin farko dake Jaen yayin da 50 kuma aka kai su Asibitin kwararru na Murtala Muhammad domin samun kulawa,” in ji shi,

Saminu ya kara da cewa kawo yanzu, ba a samu asarar rai ba a sakamakon afkuwar lamarin.

Jaridar Dimokuradiyya ta a ranar Lahadi ta gano cewa yawancin wadanda abin ya shafa mata ne da kananan yara.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy