Mutane 7 sun rasa rayukansu a hatsarin Mota a Edo

0

Mutane 7 sun rasa rayukansu a hatsarin Mota a Edo - Dimokuradiyya

Mutane 7 sun rasa rayukansu a hatsarin Mota a Edo

Kimanin mutane 7 aka tabbatar da mutuwar a hatsarin mota a Agbede na Ƙaramar Hukumar Etsako ta Jahar Edo.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Kwamanda mai kula da Hanyoyi, kuma Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Hukumar Kula da Haɗurran Kan Hanya Miss Omozie Inegbenebor Jahar Edo.

Inegbenebor tace hatsarin Wanda ya faru a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 11 na dare, ya rutsa da Ababen hawa 14, da ya haɗa da manyan motoci 13 da mota sienna guda ɗaya.


Download Mp3

Tace Manyan mutane 25 hatsarin ya rutsa dasu, a yayinda mutane 7 suka mutu, da Jikkata sauran mutanen.

Tace hatsarin wanda ya faru, a Agbede kilomita 20 daga mazaunin Hukumar FRSC a Agbede, ya faru ne saboda rashin birki na motocin da suka hau sauran motocin dake tsaye, wanda ya haddasa hatsarin da Gobara.

“Jami’an Hukumar masu aiki ceto na FRSC a Edo tuni suke a wurin suna cigaba da aiki, suna cigaba da gyara hanya da kula da Ababen hawa.

“Kwamandan shiyya Mr. Henry Benamaisia a lokacin da yake ƙididdiga akan yanayin hatsarin,ya Jajantawa iyalan da lamarin ya shafa da suka halarci wurin.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy