Mutane na Jiran su Saida Ƙuri’un su a Zaben Gwamnan Osun — Malamin Kirista
Mutane na Jiran su Saida Ƙuri’un su a Zaben Gwamnan Osun
Shugaban Kwamitin Zaman Lafiya a Osun Rabaran Father Atta Barkindo ya bayyana damuwa akan sayen ƙuri’u gabanin Babban Zaɓen ranar 16 ga watan Juli na Gwamnan a Jahar Osun.
A lokacin da yake jawabi ga Manema labaru a gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba, Malamin Kiristan yace masu kaɗa ƙuri’a a Osun a shirye suke domin su saida ƙuri’un su a lokacin zaɓe.
Barkindo wanda shine babban Darakta a cocin Kuka ya bayyana damuwa na talauci a kasa, yana mai cewa magance matsalar saida kuri’a yafi a tsaya ana magana akan sa.
Barkindo yace dole a magance matsalar saida kuri’a.
Yace “mun yi ta gudanar da taro na gama gari, kuma mun bayyana a rediyo , da gidan talabijin a Osun domin kira ga Al’umma da kada su saida ƙuri’un su.
“Dubu uku da za’a baka, ba komai bace gareka da iyalan ka, bazai riƙe ku sati guda ba. Muna kokari muga mun hana batun saida ƙuri’un nan
“Muna kira ga Hukumomi, domin akwai matasa da yawa da basu da aikin yi, iyalai suna zama ba tare da abinci ba.
Ya bayyana damuwa na batun rashin tsaro a Jahar gabanin zaɓen.
