Na fito takaran shugaban kasa ne don na sake gogewa a siyasa— Gwamna Yahaya Bello

0

Na fito takaran shugaban kasa ne don na sake gogewa a siyasa— Gwamna Yahaya Bello - Dimokuradiyya

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce ya shiga takarar shugaban kasa a 2023 a karkashin jam’iyyar APC, domin kawai ya kara basira a matsayinsa na dan siyasa.

Duk da cewa ya sha kaye a zaben fidda gwanin da ya samar da tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa, Bello ya ce darussan da aka koya daga fafatawar sun hade da kyau kuma za su yi amfani a harkokin siyasa na gaba.

Gwamnan ya yi wadannan kalamai ne jim kadan bayan ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Larabar, domin yi masa godiya bisa yadda ya bayar da dama ga daukacin ‘yan takara a daidai lokacin zaben fidda gwani da aka gudanar kwanan nan.


Download Mp3

Idan dai za a iya tunawa, a yayin da ake ta kara takun-saka kan wanda zai fito a matsayin dan takarar jam’iyya mai mulki, Bello ya tsaya tsayin daka kan cewa ba zai janye wa kowane dan takara ba.

Rahotanni sun bayyana cewa ya fice daga taron masu ruwa da tsaki da ya hada da Gwamnonin APC daga Arewa inda ya dage cewa Shugaban kasa ne kawai iya tilasta masa ya sauya daga matsayarsa na taka takara ga duk wani mai son tsayawa takara.

Daga baya an gan shi ya ziyarci Tinubu domin bayyana cikakken goyon bayansa ga burinsa na zama shugaban kasa har ma ya bayar da cikakken ofishin yakin neman zabe domin taimakon mai rike da tutar takarar shugaban kasan a inuwar Jam’iyar APC.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy