Na Shiga Mummunan Tashin Hankali Da Naga Sanatocin APC Na Ficewa Daga Jam’iyar—- Abdullahi Adamu

0

Na Shiga Mummunan Tashin Hankali Da Naga Sanatocin APC Na Ficewa Daga Jam’iyar—- Abdullahi Adamu - Dimokuradiyya

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Abdullahi Adamu, ya bayyana damuwarsa dangane da yadda ake yawan sauya sheka a jam’iyyar.

Sanatoci bakwai sun fice daga APC zuwa wasu jam’iyyun adawa bayan sun kasa samun tikitin jam’iyyar da ke mulki a zaben 2023.

Mambobin Majalisar Dattawan da suka fice daga APC sun hada da Ibrahim Shekarau (Kano), Yahaya Abdullahi (Kebbi) Adamu Aliero (Kebbi), Dauda Jika (Bauchi), Ahmad Babba Kaita (Katsina), Lawal Yahaya Gumau (Bauchi), da Francis. Alimikhena (Edo).

Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawar sirri da Sanatocin APC, Adamu ya ce abin takaici ne yadda ‘yan majalisar suke fice wadaga jam’iyyar.

Ya ce ana sauya shekar ne saboda kakar zabe da aka saba gani a kasar.

Ya ce: “A kowace shekara ta zaɓe, irin waɗannan matakan biyan kuɗi na ba da damar mutane, masu ruwa da tsaki su yi irin wannan aiki.

“Saboda haka, ba na yi wa abin da ke faruwa a wasu jam’iyyun ba, na damu da abin da ke faruwa a jam’iyyarmu.

“Kun san ba a APC kadai ake yin wannan abu ba. Domin mu ne jam’iyya mai mulki, matsalolinmu sun fi fitowa fili a idon jama’a.

“Babu wani shugaban da ke da alhakin da ba zai damu da rasa memba daya ba, ba maganar biyu ko uku ba.

“A halin yanzu muna fuskantar matsalolinsu amma mun jajirce tare da takwarorina na Kwamitin zastarwa na kasa don fuskantar matsalolin da kuma magance su cikin yardar Allah.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy