Nan Bada Jimawa Ba Bola Tinubu Zai Lashe Tikitin Takarar shugaban kasa A APC – Ganduje

0

Nan Bada Jimawa Ba Bola Tinubu Zai Lashe Tikitin Takarar shugaban kasa A APC – Ganduje - Dimokuradiyya

Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje yace suna da kyakkyawan fatan cewa Jagoran Jam’iyyar APC Ahmed Bola Tinubu ne zai lashe zaben fidda gwanin dan Takarar shugaban kasa da ake ci gaba da yi yanzu haka a Abuja.

Ganduje Ya Bayyana hakan ne a filin eagles square dake Abuja, wanda yace da dukkan alamu dangane da yadda zaben yake gudana, Tinubu shine akan gaba, kuma wanda yafi kowa samun jama’a da kuri’a mai rinjaye.

Ya ce a matsayin su na gwamnonin arewa tuni suka bayyana matsayar su ga shugaban kasa Muhammad Buhari, cewa sun amince mulki ya koma ga dan kuma a cewar sa tuni ya amsa nace da wannan kuduri nasu.


Download Mp3

Ganduje Ya ce a yadda Deliget ke ci gaba da ruwan Kuri’a a zaben dan takarar shugaban kasar na APC, hakan ya nuna irin Dattakun Jagaban Borgu.

Kazalika ya bayyana gamsuwar sa dangane da yadda zaben ke gudana, inda yace yadda aka yi fatan ya kasance a haka yake tafiya.

Da dama dai cikin yan takarar tuni suka janyewa Tinubu tare da sanar da mara masa baya, a fatan da suke na ganin ya dare kujerar.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy