Nan da mako biyu za’a kammala layin dogo na Apapa—- Gwamnatin Tarayya

0

Nan da mako biyu za’a kammala layin dogo na Apapa—- Gwamnatin Tarayya - Dimokuradiyya

Karamar Ministar Sufuri ta Najeriya, Sanata Gbemisola Saraki, a yau Litinin ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa, nan da makonni biyu za a kammala titin jirgin kasa da ya hada tashar jirgin ruwa ta Apapa.

Saraki ta bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da ta jagoranci wasu jami’an ma’aikatar sufuri ta tarayya zuwa tashar ruwa ta Apapa ta tashar jirgin kasa ta Mobolaji Bank Anthony da ke Legas.

Ta ce manajan aikin na kamfanin gine-gine na kasar Sin (CCECC), Mista Xia Lijun, ya ba ta tabbacin cewa za a kammala aikin da aka fara nan da makonni biyu masu zuwa.

“Kamar yadda kuke gani, ginin na Hukumar Scanner na Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) yana bukatar a rushe shi amma an samu matsala a cikinsa.

“Ina iya ganin halin da ake ciki kuma bayan dawowata Abuja, ma’aikatar za ta gana da mahukuntan hukumar Kwastam da Hukumar Kula da Tashoshin Ruwa ta Najeriya (NPA).

“Kafin karshen mako mai zuwa, za a samar da mafita don inganta ginin titin jirgin kasa na Apapa kuma layin dogo zai fara aiki nan da makonni biyu,” in ji Saraki.

Saraki, ta yi nuni da bukatar ruguza cibiyar na’urar daukar hoto ta Kwastam.

Ta kara da cewa Da yuwuwar jami’an ma’aikatan su sake komawa domin tabbatar da cewa an sanya na’urar daukar hoto don tabbatar tsaro. (NAN).

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy