- Advertisement -

Osibanjo Zai Wakilci Buhari a Taron ECOWAS karo na 61 a Ghana

0

Osibanjo Zai Wakilci Buhari a Taron ECOWAS karo na 61 a Ghana - Dimokuradiyya

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo zai wakilci najeriya yayin taron kungiyar ECOWAS da za a gudanar a kasa Ghana karo na 61.

- Advertisement -

Mai magana da yawun sa Laolu Akande ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, inda yace mataimakin shugaban kasar zai bar najeriya ne a yau, kuma zai wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin taron.

Taron dai zai gudana ne a gobe Lahadi, wanda kuma shugabannin kasashen dake karkashin kungiyar, ake sa ran suma su halarci taron, wanda zai mayar hankali kan ayyukan agaji, tsaro a yankin kasashen da sauran batutuwa.

A dai yayin taron nan bana zai mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi kasashen Mali, Guinea, Burkina Faso, tare da lalubo hanyoyin da suke ganin zasu taimaka wajen komawa tsarin Dimokuradiyya.

- Advertisement -

Ana sa ran kuma kungiyar zata yi duba kan batutuwan matsalar rashin aikin yi da sauran kalubalen da matsa ke fuskanta, dama wasu cutuka dake wasu wasu kasashen dake karkashin kungiyar.

Dimokuradiyya ta rawito cewa a ranar 4 ga watan Yumni, shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya kai ziyara kasar Ghana, inda nan ma ya halarci wani taro da aka gudanar kan halin da kasashen yammacin Africa ke ciki, dama batun kasashen dake karkashin juyin mulki.

- Advertisement -
wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy