PDP ta sake sanya ranar da zata gudanar da Zaɓen Fidda Gwani a Katsina, Lagos, Imo, Benue

0

PDP ta sake sanya ranar da zata gudanar da Zaɓen Fidda Gwani a Katsina, Lagos, Imo, Benue - Dimokuradiyya

PDP ta sake sanya ranar da zata gudanar da Zaɓen Fidda Gwani a Katsina, Lagos, Imo, Benue

Jam’iyyar PDP ta amince da sake gudanar da Zaben Fidda Gwani a Jahohin Lagos, Imo, da Benue, da Katsina.

A cikin wata sanarwa da mai kula da harkokin Jama’a na PDP Debo Olugunagba ya Fitar a ranar Asabar, ya bayyana cewa Jam’iyyar ta ɗauki wannan matsaya bayan yin karatu akan rahoton da Kwamitin Zaɓe da na Ɗaukaka Ƙara suka shigar a Jahohin.

Wuraren da aka amince a sake zaɓen fidda Gwani sun hada da Mazaɓar Ahiazu da ta Orsu a Jahar Imo, zai wakana a ranar 5 ga watan yunin Shekarar 2022.


Download Mp3

A yayin mazabun Musawa, da Zango, da Dandume a Jahar Katsina, da Mazaɓar Tarayya ta Oru ta Gabas, da Orsu da Orlu na jahar Imo, da Mazaɓar Tarayya ta Kwande/Ushongo na Jahar Benue duk za’a gudanar dasu a ranar Lahadi 5 ga watan Yuni na Shekarar 2022.

Zaɓen Fidda Gwani na Ɗan Majalisar Wakilai ta Ƙasa na Lagos (Mazaɓu 24) za’a gudanar dashi a ranar Litinin 6 ga watan Yuni na Shekarar 2022.

Sanarwar tace “Zaɓen Fidda Gwanin Dan Majalisar Dattijai na Kaduna ta Tsakiya, da Enugu ta Yamma, da Ɗan Majalisar Wakilai na Boki/Ikom, da Yakuur II dukkanin su a Jahar Cross River da aka sanya za’a gudanar a ranar 4 ga watan Yunin Shekarar 2022 an soke shi.

“Dukkanin Ƴan Jam’iyyar da lamarin ya shafa ana kira a garesu dasu san da haka.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy