PDP za ta bayyana abokin takarar Atiku cikin sa’o’i 48 – Ayu

0

PDP za ta bayyana abokin takarar Atiku cikin sa’o’i 48 – Ayu - Dimokuradiyya

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyiochia Ayu, a ranar Talata, ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar zata bai yana mataimakin dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar, a cikin sa’o’i 48 masu zuwa.

Ayu ya ba da wannan tabbacin ne a jawabin bude taron da ya yi da mambobin kwamitin tuntuba da aka kafa domin taimakawa Atiku wajen zaben wanda zai yi takara.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Ayu na ganawar sirri da wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a sakatariyar jam’iyyar ta kasa.

Ya bayyana cewa taron na ci gaba da tuntubar juna da nufin kaiwa ga zabin da ‘yan Najeriya za su yi murna da zabar wanda zai irike mukamin.

Ayu ya ce, “Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarmu zai zo nan ba da jimawa ba”.


Download Mp3

“Dan takarar ya rubuta mana a matsayin mu na bangaren gudanarwa na jam’iyyar kan zabin abokin takararsa.

“Saboda sashi daban-daban na jam’iyyar suna da cikakken wakilci a cikin kwamitinsa – kwamitin zastarwa na kasa, wand ya hadar da, kungiyar gwamnoni, majalisar dokoki ta kasa, da tsoffin gwamnonin da suka gabatar da ‘yan takararsu.

“sakamakon wannan shawara za ta kasance karkashin jagorancin mataimakina, Ambasada Umaru Damagum.

“Ina yi muku fatan samun nasarar shawarwarin da za ku nema, kuma ina fatan za ku cimma matsaya tsakanin gobe zuwa Juma’a.

“Dan takarar shugaban kasa, a wannan karon, ya yanke shawarar daukar kowa da kowa ba kamar 2019 ba lokacin da bai tuntubi kowa ba kan zabin abokin takararsa.”

Taron da ke gudana yana da Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP, Aminu Tambuwal; Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed; Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom; tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark; tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko; Tsohon Gwamnan Jihar Kuros Riba, Liyel Imoke, da Sanata Philip Aduda da dai sauran su.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, ta baiwa jam’iyyun siyasa har zuwa ranar Juma’a, 17 ga watan Yuni, 2022, su mika sunayen ‘yan takararsu na shugaban kasa da abokan takararsu.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy