Rarara Ya Taso Keyar Manyan Jihar Katsina Gaba AKan Matsalar Tsaro

0

A karo na biyu, fitaccen Mawakin Siyasa a Arewa, Dauda Kahutu Rarara yana ci gaba da nuna damuwarsa kan matsalar tsaron da yake addabar jihar sa ta Katsina.

Rarara dai haifaffen garin Kahutu ne, da ke karamar hukumar Danja a jihar Katsina. 

Za a iya cewa matsalar rashin tsaro a jihar Katsina ba boyayyen al’amari ba ne, wadda ita ma ta shiga a cikin jerin jihohin Arewa wadanda ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane su ke ci gaba takurawa wasu yankunan kananan hukumomi irin su, Safana, Faskari, Kankara, Batsari Jibiya, Dan Musa, Sabuwa da sauransu.

Wata biyu da suka gabata mawakin ya yi wakar farko, inda ya yi kira ga al’ummar jihar Katsina, da su hada kai babu batun dan Apc ko PD. A cewar sa, matsala ce da ta addabi kowa don haka sai an hadi kai.

Related Post:-

A sabuwar wakar da mawakin ya fitar kashi ta biyu, ya fara da lissafa sunayen Fitattun Jihar, tun daga kan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, da manyan masu kudi da ‘yan Kasuwa, da ma’aikatan Gwamnati wanda akalla ya lissafa sama da mutum 35 wanda duk duniya ta san su kuma ‘yan jihar Katsina ne.

A cewar Rarara, Manyan Jihar sun zura ido suna gani za a ga bayan talakawa, amma ba su ce komai ba, kuma suna da damar da za su ceci al’umma amma sun yi gum da bakin su.

Wakar ta sa dai za a iya kiran ta kan mai uwa da wabi, domin bai ware ‘yan jam’iyyar APC ko PDP ya dorawa wani laifi ba. Wakokin Rarara na Matsalar Tsaro, sun sha bamban da sauran  irin wakokin da aka saba jin yana yi, musamman zargin sukar ‘yan adawa da ya saba yi.

Hatta ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP, wadanda ba su sauraren wakokin mawakin, a wannan karon suna yabon sa saboda yadda ya nuna damuwar sa akan halin da Talakawan jihar Katsina su ke ciki.

Wakar ta sa mai tsawon mintuna 32 da dakika 22 ya sanya mata suna da “Jihata Jihata Ce”

Ku Tura Zuwa Facebook WhatsApp Twitter Instagram Da Telegram.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Sharing is Awesome, Do It!

Share this post with your friends
close-link