- Advertisement -

Reno Omokri ya yiwa Jam’iyyar LP Shaguɓe, yace kasa da mutane 500 suka halarci taron Obi na Osun

0

Reno Omokri ya yiwa Jam’iyyar LP Shaguɓe, yace kasa da mutane 500 suka halarci taron Obi na Osun - Dimokuradiyya

Reno Omokri ya yiwa Jam’iyyar LP Shaguɓe, yace kasa da mutane 500 suka halarci taron Obi na Osun

- Advertisement -

Mai sharhi kan Siyasa Reno Omokri yace ƙasa da mutane 500 suka halarci gangamin yaƙin neman zaɓe na Jam’iyyar Labour Party, gabanin Babban Zaɓen Gwamna na ranar Asabar a Jahar Osun.

Jam’iyar Ta gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓe a ranar Laraba ga Lasun Yussuf, Ɗan Takarar Jam’iyyar. Peter Obi ya samu halarta.

A lokacin da yake kira ga ƴan Jahar da kada su saida ƙuri’a, Obi ya shawarce su da u karɓi kuɗi ga Masu sayen ƙuri’u, sannan su zaɓi Jam’iyyar Labour Party.

- Advertisement -

Yace Yusuf ya cancanta ya zama Gwamnan Jahar Osun na nan gaba.

Da yake maida jawabi, bayan Gangamin yaƙin neman zaɓe, Omokri yace “a takaice mutane da yawa sun halarci gangamin yaƙin neman zaɓe. Idan zagi da gargaɗi za’a maida su ƙuri’u. Oya, ku zageni.

Da yake jawabi ƙarƙashin rubutun sa na Twitter, wani ya rubuta “kai sakarai ne. Babu wani daya tura mutane da yawa.”

- Advertisement -

“Kai baka tunani zagi, kamar naka, shine dalilin daya sanya ƙasa da mutane 500 suka halarci taron Jam’iyyar ku a Osun? Omokri ya maida jawabi.

A juma’ar data gabata ne, Omokri yace duk abinda ya faru a gareshi to a ɗora laifin ga Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar Labour Party.

- Advertisement -
wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy