Saboda wariya, ‘yan Kannywood sun ƙaurace wa Bikin Bajekolin Finafinai na Zuma

0

Saboda wariya, ‘yan Kannywood sun ƙaurace wa Bikin Bajekolin Finafinai na Zuma

Dakta Ahmad Sarari (a hagu) da Alh. Sani Sule Katsina

MANYAN ƙungiyoyi biyu da ke wakiltar masu shirya finafanan Hausa sun barranta kan su daga shiga Bikin Bajekolin Finafinai na Zuma (Zuma Film Festival) na bana wanda ke gudana a Abuja yanzu haka.

Hukumar Finafinai ta Nijeriya (Nigerian Film Corporation, NFC) ita ce ke shirya bikin a duk shekara inda ta kan yi haɗin gwiwa da ƙungiyoyin ‘yan fim na Arewa da na Kudu domin samun halartar kowa da kowa.

Amma a bana an samu ɓaraka, inda Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (Motion Picture Practitioners Association of Nigeria, MOPPAN) da kuma Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Arewacin Nijeriya (Arewa Filmmakers Association of Nigeria, AFMAN) su ka aika da buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Ministan Yaɗa Labarai, Alhaji Lai Mohammed, su ka faɗa masa ƙudirin su na ƙaurace wa bikin a bisa wasu ƙwararan dalilai.

A cikin wasiƙar, mai ɗauke da sa hannun shugabannin ƙungiyoyin biyu, Dakta Ahmad Sarari (MOPPAN) da Alhaji Sani Sule Katsina (AFMAN), ƙungiyoyin sun bayyana cewa sun ƙaurace wa bikin ne saboda an nuna masu wariya a matsayin su na Musulmi kuma ‘yan Arewa.

Su ka ce dalili na ɗaya shi ne an saka bikin a ranar Sallah, ranar da Musulmi a faɗin duniya su ke shagulgula, sannan kuma ma ranar hutu ce da gwamnati ta ware don nuna girmamawa da murna ga wata mai tsarki na Ramalana.

Su ka yi nuni da cewa waɗannan dalilan sun sa dukkan Musulmi ba su shiga bikin don amfana da shi ba.

Ƙungiyoyin su ka ce su na tantamar idan wata hukuma ta gwamnati za ta iya shirya irin wannan taron na ƙasa baki ɗaya a lokacin Kirsimeti ko kuma lokacin bikin sabuwar shekara.

Dalili na biyu na ƙungiyoyin shi ne a ranar 16 ga Fabrairu, 2022, hukumar ta NFC ta naɗa shugaban MOPPAN, Dakta Sarari, a matsayin shugaban ƙaramin kwamitin shirya bikin (LOC) na shiyyar Kano, shi da membobi biyu, waɗanda za su kula da yankin Arewa don shiga bikin.

Ministan Yaɗa Labarai, Alhaji Lai Mohammed

Su ka ce wasiƙar naɗin ta umarci kwamitin da ya tura da bayanan shawara, kuma ba tare da ɓata lokaci ba kwamitin ya cika umarnin NFC, ya aika da dukkan muhimman bayanan da ake buƙata, har da sauran ayyukan.

Su ka ce amma daga lokacin har zuwa yanzu kwamitin bai samu amsa daga masu shirya bikin ba, ga shi kuwa NFC na ta haƙilon wallafa labarai da sanarwa a jaridu, har da faɗin wai ‘yan Kannywood ma su na cikin masu shirya bikin.

Ƙungiyoyin sun bayyana mamaki kan yadda aka ci gaba da aikin shirya gasar tare da takwarorin su da ke kudancin ƙasar nan, waɗanda su ka kira da ‘yan Legas.

Ƙungiyoyin sun bada dalili na uku, inda su ka ce NFC ta aika da wasiƙa zuwa ga ɗaya daga cikin dattawan Kannywood, wanda ake ɗauka da matuƙar girma, kuma fitaccen jarumi, wato Alhaji Ibrahim Mandawari, ta sanar da shi cewa ya na ɗaya daga cikin mutanen da za a karrama a bikin a matsayin ‘gwarzon nasarar rayuwa’. Amma jim kaɗan kafin buɗe bikin sai Mandawari ya kaɗu da masu shiryawar su ka sanar da shi cewa ba ya cikin waɗanda za a karrama ɗin, saboda haka an cire sunan sa daga cikin jerin su, ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba. Amma sai ga shi waɗanda aka zaɓa daga sauran sassa na ƙasar nan an karrama su ɗin.

Gamayyar masu shirya finafinai daga Arewa ɗin sun roƙi ministan da ya shiga cikin lamarin, ya yi gyaran da ya kamata.

Mujallar Fim ta lura da cewa kusan dukkan ‘ya’yan ƙungiyoyin sun yi na’am da wannan mataki da shugabannin su su ka ɗauka.

Ɗaya daga cikin dattawan Kannywood, Alhaji Mohammed Kabiru Maikaba, ya ce, “Mu dattawan masana’antar Kannywood, a ƙarƙashin ‘Kannywood Foundation’ da ‘Kannywood Elders Forum’, na farin ciki, kuma mu na bada cikakken goyon bayan mu kan wannan kyakkyawan mataki da shuwagabannin katafanin ƙungiyoyin wannan masana’anta guda biyu su ka ɗauka.

“Mu na goyon baya, mu na tare da ku bisa yanke nasabar shiga bikin finafinai na Zuma wanda ya ke gudana yanzu.

“Mu na nan mu na sauraren matakin da Ministan Yaɗa Labarai da hukumomin shirya wannan biki za su ɗauka don mu ma mu bada tamu gudunmawar don tabbatar da mun tafi tare mun tsira tare.

“Mu na taya ku addu’a da Allah ya ci gaba da yi maku jagora. Kuma mu na roƙon Allah ya ci gaba da ɗinke kawunan mu don mu kasance uwa ɗaya uba ɗaya ala kulli halin.”

Shi kuwa dattijon industiri Malam Khalid Musa cewa ya yi, “Ina ganin ya kamata mu dawo da ‘MOPPAN Awards’, kuma mu fifita ta sama da kowacce a Nijeriya. Akwai ‘MOPPAN Awards’ da aka fara, an yi kusan kashi biyu zuwa uku. ‘It doesn’t matter who (is the) organiser once we owned it in our best interest’.”

Shi kuma fitaccen darakta Falalu Ɗorayi cewa ya yi, “Abin da ya ba ni mamaki a irin wannan lokacin, kuma duk da ya faru amma a sanar saboda a ɗan yi wani motsi a ɗaga wa mutanen nan hankali. Kullum fa in mu ka zama soloɓiyo, babu abin da za a yi da mu, wallahi tallahi.

“Ya kamata mu sani, mu na da ƙarfi, mu na da ‘power’, ya kamata kullum mu riƙa motsawa. Su fa (‘yan Kudu) ɗan abu kaɗan fa za su yi ‘protest’ a soshiyal midiya a saurare su. Mun yarda a bi ‘due process’, amma wani lokacin in mu na so a kalle mu da darajar da mu ke so, waɗanda su ke riƙe da muƙaman nan a Abuja su kalli Kannywood da shi, wallahi sai mun fita daga inda ku ke tunani. Ni dai ina fatan a yi wani motsi wanda ya fi wannan.”

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy