Sabon Rikici: Manoma 2 Sun Bakunci Lahira A Jihar Benue

0

Sabon Rikici: Manoma 2 Sun Bakunci Lahira A Jihar Benue - Dimokuradiyya

Rahotanni sun ce an kashe manoma biyu a wani sabon hari da aka kai a unguwar Ikyungwa Tombo, kusa da al’ummar Ayilamo a karamar hukumar Logo a jihar Benue.

Jaridar Daily Trust ta ruwiato cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin da karfe 5 na yamma yayin da su biyun ke dawowa daga gonakin su.

An bayyana sunayen wadanda suka mutun a matsayin Bem Uhembe da Mungwa Zuzu, dukkansu ‘yan kauyen Tse Ibor ne da ke komawa garin Ayilamo bayan sun yi aikin gonakinsu, saboda zargin wasu da ake zargin makiyaya ne sun ace Iko da matsugunan su.


Download Mp3

Mutanen yankin sun ci gaba da cewa an ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiye gawa na Ayilamo.

Shugaban karamar hukumar, Aber Terse, ya tabbatar wa wakilin Jaridar Daily Trust ta wayar tarho cewa, wadanda suka mutu – wata macace da namiji – an yi musu dirar mikiya tare da kashe su bayan sun bar gonakinsu da yammacin ranar Litinin.

Aber ya zargi makiyayan da laifin kisan mutanen biyu sakamakon mamayar unguwar Tombo, wani wurin noma, wanda wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton makiyaya ne ke ci gaba da kai musu hari tun a shekarar 2016.

Da aka tuntubi jami’ar hulda da jama’a na ‘yan sanda jihar ta Benue SP, Catherine Anene, ta ce ba ta samu rahoton faruwar lamarin ba.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy