Sanata Uba Sani Ya Taya Sani Kila murnar samun muƙamin Kwanturola na Immigration

0

Sanata Uba Sani Ya Taya Sani Kila murnar samun muƙamin Kwanturola na Immigration - Dimokuradiyya

Sanata Uba Sani Ya Taya Sani Kila murnar samun muƙamin Kwanturola na Immigration

Sanata Uba Sani ya bayyana haka ne a cikin wani sakon sa na taya murna daya fitar a yau juma’a Uba Sani.

Dan Takarar Gwamnan Jihar Kaduna Karkashin jam’iyar APC Yace “A ranar Laraba takwas 8 ga watan Yuni, 2022, na sami karramawa da halartar bikin Ƙarin girma na Sani Liman Kila wanda kwanan nan ya samu Ƙarin Girma zuwa mukamin Kwanturola na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS).

Sanatan Ya Ƙara da cewa Sani Kila ya kasance fitaccen abin misali kuma hazikin mutun ne da kwazo a Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya (NIS).


Download Mp3

“Da yake na san shi kuma na yi aiki da shi shekaru da yawa, zan iya gaya muku fiye da kowa ko wanene babban jami’in Ƙaunar sa da sadaukarwa tare da da nuna girmawa ga aikin sa da Kuma ƙasa baki daya”.

“Ina taya shi murna da wannan ci gaba da ya samu kuma ina yi masa fatan alheri a cikin ayyukansa na yanzu da Kuma na gaba”. Inji Sanata Uba sani

Sanata Uba Sani shine Ɗan takarar Gwamna Mafi ƙarfi da samun Kwarjinin jama’a a duk cikin ‘yan takarar da jam’iyar APC ta tsayar a arewacin nageriya.

Matasa Maza da mata na yawan fa’din kirkin Sani Kila musamman a fannin taimakon Matasa a cikin Hukumar ta kula da Shige da ficen Nageriya.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy