- Advertisement -

Sanata Uba Sani ya zaɓi Mataimakiyar El-Rufa’i, Hadiza Balarabe a matsayin abokiyar takarar sa

0

Sanata Uba Sani ya zaɓi Mataimakiyar El-Rufa’i, Hadiza Balarabe a matsayin abokiyar takarar sa - Dimokuradiyya

Sanata Uba Sani ya zaɓi Mataimakiyar El-Rufa’i, Hadiza Balarabe a matsayin abokiyar takarar sa a Kaduna

- Advertisement -

Sanata Uba Sani kuma Ɗan Takarar Gwamnan Jahar Kaduna ya zaɓi Mataimakiyar Gwamna El-Rufa’i, Hadiza Balarabe a matsayin wadda za tayi mashi Mataimaki a Takarar Gwamnan Jahar Kaduna a Babban zaɓen Shekarar 2023.

Sanata Uba Sani Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Kaduna Ƙarƙashin Jam’iyar APC a zaɓen 2023 ya bayyana hakan ne yau a wata sanarwa a shafinsa na Facebook.

Yana mai cewa “bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jihar Kaduna, ina mai farin cikin sanar da cewa na zaɓi mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe a matsayin mataimakiya ta a zaben gwamnan jihar Kaduna a 2023”

- Advertisement -

“Dr. Hadiza Balarabe ta bada gudunmawa sosai ga gagarumin ci gaba da gwamnatin Mallam Nasir El-Rufai ta samu, a fannin samar da ababen more rayuwa da kuma ci gaban jama’a”. Inji Sanata Uba Sani

Ya ƙara dacewa “Dakta Balarabe ta nuna ƙwazo da aiki a kan lokaci, sadaukarwa da kuma aiki, wajen sauke nauyin da aka ɗora mata na Mataimakiyar Gwamna wanda ya ƙara mata daraja ga masu ruwa da tsaki a Jihar”

“Don haka ina kira ga al’ummar Jihar Kaduna masu daraja da su goyi bayan zabin Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe a matsayin mataimakiya ta. Ina kuma kiran su da su fito cikin jama’a don kaɗa ƙuri’ar zaɓen wannan haɗi namu yayin Babban Zaɓen 2023, hakan zai bamu damar gina jihar Kaduna cikin lumana da wadata da kuma zuwa matakin cigaba”.

- Advertisement -

A tare, mun Ƙudiri aniyar sanya Jiha ta zama maudu’in shugabanci nagari da kuma rikon amana.Inji sanata Uba Sani.

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy