Sarkin Kano Ya Ɗaga Likkafar Masallacin Jami’ar MAAUN Zuwa Na Juma’a

0

Sarkin Kano Ya Ɗaga Likkafar Masallacin Jami’ar MAAUN Zuwa Na Juma’a - Dimokuradiyya

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya ɗaga Likkafar masallacin Kamsu Salawati n jami’ar Maryam Abacha dake Kano Nigeri, zuwa matsayin masallacin Juma’a.

Sarkin ya sanar da ɗaga Likkafar masallacin ne a lokacin da kwamitin masallacin karkashin jagorancin Farfesa Mohammad Israr, inda suka kai masa ziyarar ban girma a fadarsa a yau Talata.

Sarkin Kanon wanda ya yi magana ta bakin Wazirin Kano, Alhaji Sa’ad Muhammad, ya ce inganta masallacin daga masallacin salloli biyar zuwa masallacin Juma’a zai ba dalibai damar gudanar da sallar Juma’a ba tare da yin tattaki zuwa wurare masu nisa don halartar sallar ba.

Ya kuma bukaci mahukuntan jami’ar da su tabbatar da bin duk ka’idojin da suka shafi kafa masallacin Juma’a kamar yadda Shari’a ta tanada.

Sarkin ya yabawa wanda ya assasa jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa kafa masallacin.

Majalisar limaman masallatan Juma’a na jihar ta kuma amince da matakin da sarkin ya dauka na daukaka masallacin zuwa matsayin masallacin Juma’a.

Tun da farko a nasa jawabin, Hakimin Kawo Alhaji Kabiru Garba wanda ya jagoranci kwamitin masallacin zuwa fadar, ya ce masallacin ya cancanci wannan karramawa domin jami’ar ta bi tsarin da ya dace na kafa masallacin Juma’a ta fuskar nesa da masallacin.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy