Shugaban Majalisar Dattawa Ya Roƙi Ma’aikatan majalisun dokoki kan su janye Yajin aikin da suke

0

Shugaban Majalisar Dattawa Ya Roƙi Ma’aikatan majalisun dokoki kan su janye Yajin aikin da suke - Dimokuradiyya

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan ya roki ma’aikatan majalisun kasar nan kan su janye yajin aikin da suke wanda suka fara shi a farkon Makon nan.

Sanata Lawan ya bukace su da su koma tattaunawar fahimtar juna tsakanin da mahukunta dake kula da su, don a cewar sa yajin aikin ba zai zama mafita.

Ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawa ta musamman da suka gudanar da wakilan kungiyar Ma’aikatan majalisun, da nufin duba kan yadda zasu magance matsalar yajin aikin.

Wadanda suka kasance yayin tattaunawar sun haɗar da mataimakin shugaban Majalisar Sanata Ovie Omo Age, da shugaban Masu rinjaye na majalisar dattawan Yahya Abdullahi, da kuma bulaliyar Majalisar Sabi Abdullahi.

Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa kungiyar ma’aikatan majalisun dokokin Ƙasa, sun tsunduma yajin aiki ne a ranar Litinin din da ta gabata, sakamakon kokawa da su kai kan alawus din su, da kuma albashi.

Bayan gama tattaunawa da bangarorin biyu ne kuma sai shugaban majalisar ya dauki alkawarin duba kan matsalar, tare da tattaunawa da bangarorin da suke da alaka da wannan batun.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy