Shugabancin Kasa 2023: Abinda Yasa Kwankwaso, Peter Obi Ba Zasu Iya Kayar Da Atiku, Tinubu Ba – Adeyanju

0

Shugabancin Kasa 2023: Abinda Yasa Kwankwaso, Peter Obi Ba Zasu Iya Kayar Da Atiku, Tinubu Ba – Adeyanju - Dimokuradiyya

Gabanin zaben 2023, an gargadi ‘yan takarar shugaban kasa irin su Peter Obi, Rabiu Kwankwaso, Omoyele Sowore da sauran ‘yan siyasa kan dalilin da ya sa ba za su iya kayar da jam’iyyar APC, da PDP, ba.

Lauyan mai fafutuka, Deji Adeyanju, ya ce Obi, Kwankwaso, Sowore, da sauransu ba za su iya kayar da Bola Tinubu da Atiku Abubakar ba idan ba su yi aiki tare ba.

Adeyanju ya yi gargadin cewa a yankunan karkara ake cin zabe ba a birane ba.

A cikin jerin sakonnin da ya wallafa a shafinsa na twitter, mai sharhin zamantakewa da siyasa ya ce ya kamata ‘yan siyasa su hadiye girman kai su yi aiki tare.

A cewar Adeyanju: “Ba yadda za a yi Peter Obi, Kwankwaso, Sowore da sauran ’yan siyasa su kayar da APC da PDP idan basu hada kai ba saboda ba a ci zabe a birane ba, sai a karkara.

“Ya kamata ‘yan siyasa su koyi hadiye girman kai su yi aiki tare.

“Wannan dole ne in zama shugaban kasa ta kowane hali shi ya sa APC da PDP za su ci gaba da kaskantar da ‘yan siyasa masu girman kai.

“Ku rungumi wannan gaskiyar don amfanin ‘yan Najeriya kuma ku yi aiki tare.”

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy