- Advertisement -

SIYASAR JIHAR KADUNA: Sanata Uba Sani ya amshi Ɗan Takarar Sanatan Kaduna ta Tsakiya

0

SIYASAR JIHAR KADUNA: Sanata Uba Sani ya amshi Ɗan Takarar Sanatan Kaduna ta Tsakiya - Dimokuradiyya

SIYASAR JIHAR KADUNA: Sanata Uba Sani ya amshi Ɗan Takarar Sanatan Kaduna ta Tsakiya

- Advertisement -

Ɗan Takarar Sanatan Kaduna ta Tsakiya Muhammad Dattijo ya kaiwa Sanata Uba Sani ziyarar Ban girma da Barka da Sallah.

Sanatan ya bayyana haka a shafin sa na Facebook.

Sanata Uba sani Yace “Ɗan uwana kuma Ɗan Takarar Sanatan Kaduna ta tsakiya a jam’iyyar APC, Muhammad Sani Dattijo ya kawo mani ziyarar gaisuwar Sallah a gidana na Kaduna”.

- Advertisement -

“Mun yi musayar ra’ayoyi kan halin da jam’iyyar APC ke ciki a jihar Kaduna, da zaben 2023 mai zuwa da ingantattun dabaru da tsarin tabbatar da gagarumar nasara ga jam’iyyar a jihar tamu ta Kaduna.

” Ina godiya ga mai girma Sanatan mu kan wannan karramawa. Tare za mu daga jihar Kaduna zuwa tudu”Inji Sanata Uba sani.

Sanata Uba Sani yanzu haka shine Ɗan takarar Gwamnan jihar kaduna Karkashin jam’iyar APC yayinda Mohammad sani Dattijo ke takarar Neman zama Sanata Kaduna ta tsakiya zuwa ga majalisar Dattijan Nageriya domin maye Gurbin Sanata Uba Sani wanda shine Sanata Mai ci a halin Yanzu.

- Advertisement -

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy