- Advertisement -

Takarar Musulmi Da Musulmi: An gargaɗi Tinubu kan ɗaukar Shettima ko Zulum

0

Takarar Musulmi Da Musulmi: An gargaɗi Tinubu kan ɗaukar Shettima ko Zulum - Dimokuradiyya

Takarar Musulmi Da Musulmi: An gargaɗi Tinubu kan ɗaukar Shettima ko Zulum

- Advertisement -

Ƙasa da makonni biyu da suka rage akan wa’adin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta INEC ta sanya, domin tura sunan Abokin takara, an gargaɗi Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC Bola Tinubu Kan ɗaukar Gwamna Babagana Umara Zulum na Jahar Borno ko kuma Kashim Shettima a matsayin Abokin takarar sa.

Anyi amanna cewar Tinubu na duba yiwuwar ɗaukar Musulmi da Musulmi duk da irin kukan da ƴan Najeriya ke yi.

Rahotanni na nuna cewa, Tinubu zai iya ɗaukar Zulum ko Shettima a matsayin abokin takarar sa, nan da wasu ƴan kwanaki.

- Advertisement -

Dan Takarar Shugaban Ƙasa ya aike da sunan Kabiru Masari a matsayin abokin takarar sa ga INEC.

Amma a yayinda lokaci ke ƙara ƙurewa, Tinubu yana cigaba da duba yiwuwar ɗaukar sunan bayan shawarwari daya nema daga masu ruwa da tsaki a bangaren siyasa.

Amma Makusancin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, Reno Omokri, yace waɗannan sunayen sune Tinubu zai zaɓi guda a cikin su, shine Zulum ko Shettima.

- Advertisement -

Tsohon Hadimin Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana irin yadda Shettima ya kasa bada tsaro ga Makarantar Kiristoci ta Chibok dake Jihar Borno.

A rubutu daya saki a shafin sa na Twitter, Omokri ya caccaki Zulum kan wulaƙantar da Al’ummar Kiristoci a Jahar sa.

Omokri yace “Dagaske matar Tinubu Fasto ce. Ba ita bace tace kada a sake yarda da Inyamurai? Idan mijinta ya ɗauki Musulmi mataimaki, irin wannan macen zata iya ajiye aƙidar ta akan Inyamurai, wanda da yawansu kiristoci ce.

- Advertisement -

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy