- Advertisement -

Tinubu-Shettima: Yanzu APC ta zama ta Ƴan Ta’adda — HURIWA

0

Tinubu-Shettima: Yanzu APC ta zama ta Ƴan Ta’adda — HURIWA - Dimokuradiyya

Tinubu-Shettima: Yanzu APC ta zama ta Ƴan Ta’adda — HURIWA

- Advertisement -

Ƙungiyar Kare Hakkin Ɗan Adam ta Najeriya HURIWA ta ayyana Jam’iyya mai Mulki a matsayin Jam’iyyar ƴan ta’adda.

A cewar Ƙungiyar, yanzu lokaci da kowane Ɗan Najeriya mai kishi zai jefar da APC a Babban Zaɓen Shekarar 2023.

Wannan ya biyo bayan Shettima ya zama mataimakin Bola Tinubu a matsayin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC.

- Advertisement -

A cewar HURIWA, Shettima ba komai bane illa mai tsananin zafin Addini kuma wanda ya tsani kiristoci, yana mai bayyana ɗaukar sa a matsayin rashin kishi, rashin bin kundin tsarin mulkin ƙasar, kuma wani abu da ke nuna cewa masu tsananin kishin addini da ƴan Ta’addan BOKO Haram da ISWAP sun karbe iko da APC.

HURIWA ta gayawa ƴan Najeriya cewa duk wata ƙuria da aka jefa wa APC an jefa ta ne domin rushewar Najeriya, suna cewa dole mutum ya zabi sauran ƴan Takara.

HURIWa yace Takarar Musulmi da Musulmi dake tafiya a Kaduna ya nuna cewa irin haka baya baiwa Kiristoci dama.

- Advertisement -

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy