- Advertisement -

Tsadar Rayuwa: Da Karfe Tsiya Masu Zanga-Zanga Sun Kutsa Kai Gidan Gwamnatin Sri Lanka

0

Tsadar Rayuwa: Da Karfe Tsiya Masu Zanga-Zanga Sun Kutsa Kai Gidan Gwamnatin Sri Lanka - Dimokuradiyya

Dubban masu zanga-zanga sun mamaye gidan shugaba Gotabaya Rajapaksa da ke babban birnin kasar Sri Lanka.

- Advertisement -

Masu zanga-zangar daga sassa daban-daban na kasar sun yi tattaki zuwa Colombo suna neman ya yi murabus bayan shafe watanni ana zanga-zangar tabarbarewar tattalin arzikin kasar.

Rahotanni sun ce tuni aka dauke shi zuwa wani wuri mafi aminci.

Kasar dai na fama da hauhawar farashin kayayyaki da kuma fafutukar shigo da abinci da man fetur da magunguna daga kasashen waje.

- Advertisement -

Dubban masu zanga-zangar adawa da gwamnati ne suka yi tattaki zuwa babban birnin kasar, inda jami’ai suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa wasu ma sun ba da umarnin “umartar” jiragen kasa da su isa wurin.

Sun kutsa cikin gidan gwamnatin Colombo, suna ta rera taken “Gota ka koma gida!” tare da keta shingaye da dama na ‘yan sanda domin isa gidan shugaba Rajapaksa.

Yan sanda sun yi ta harbe-harbe ta iska tare da yin amfani da hayaki mai sa hawaye don hana cunkoson jama’a mamaye gidan, amma sun kasa hana wasu daga cikin jama’ar shiga.

- Advertisement -

Wata majiyar tsaro ta shaida wa AFP cewa, “An raka shugaban kasar zuwa wani wurin domin tsira.” “Har yanzu shi ne shugaban kasa, rundunar soji na kare shi.”

Kazalika daga bisani Akalla mutane 33 da suka hada da jami’an tsaro ne suka jikkata kuma suna jinya a asibitin kasar Sri Lanka da ke Colombo, kamar yadda kakakin asibitin ya shaida wa sashen Sinhala na BBC.

A wani labari kuma na daban.

- Advertisement -

Gwamna Abdulrazaq Da Saraki Sun Yi Kacibus A Masallacin Idin Ilorin

A karon farko cikin shekaru hudu Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara da tsohon shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki sun yi musabaha a filin sallar idi na Ilorin.

Da yawa daga cikin masu ibada sun yi mamaki lokacin da gwamnan ya je wurin Saraki ya mika hannunsa.

- Advertisement -

Tsohon mai matsayi na uku a kasar nan ya mayar da martani kuma dukkan mutanen sun yi musanyar gaisuwa.

Da gwamna ya isa filin sallah, kai tsaye ya nufi sashin da aka tanadar masa ya zauna.

Jim kadan ya mike tsaye ya nufi inda Saraki yake zaune ya gaishe shi, suka yi musabaha.

- Advertisement -

Hakan ya jawo tsawa daga masu ibada a sashe na musamman VIP, inda suka tashi tsaye domin su hango shugabannin siyasa.

Daga nan sai gwamnan ya yi gaba da gaisawa da sauran shugabanni, musamman tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Alhaji Abubakar Kawu Baraje, aminin Saraki.

Sauran wadanda suka halarci filin Sallar Idi sun hada da tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, Mai Shari’a Moddibo Alfa Belgore.

- Advertisement -

Bayan wannan tataburzan, daya daga cikin ’yan kwamitin shirya taron a filin idin ya yaba wa gwamnan bisa nuna iya jagoranci.l na gari

Saraki, wanda shi ne Wazirin Ilorin, ya iso filin sallah tun da farko tare da mukarrabansa da sauran manyan baki.

Saraki da Abdulrazaq, wadanda suke jam’iyyu daban-daban, sun yi ta fafatawa a shekarun baya.

- Advertisement -

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy