- Advertisement -

Tsaron Yanki: Buhari Ya Godewa Kasar Portugal Domin Tallafawa Harkar Tsaro

0

Tsaron Yanki: Buhari Ya Godewa Kasar Portugal Domin Tallafawa Harkar Tsaro - Dimokuradiyya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a daren ranar Alhamis din nan ya nuna jin dadinsa ga kasar Portugal bisa tura makamai da horar da jami’an soji domin tabbatar da zaman lafiya a nahiyar Afirka.

- Advertisement -

Mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ya ce Buhari ya yi wannan yabon ne a wajen wata liyafar cin abinci da aka gudanar a fadar Ajuda, Lisbon, babban birnin kasar Portugal.

Buhari ya yaba wa shugaban kasar Marcelo Rebelo de Sousa bisa yadda ya tura dakaru domin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, da sanya ido kan harkokin siyasa da kuma ba da taimako ga wasu kasashen Afirka da suka hada da Equatorial Guinea, Cape Verde da Mozambique.

Shugaban ya ce a wajen liyafar cin abincin dare da shugaban majalisar dokokin kasar Portugal, Augusto Santos Silva, da firaminista Antonio Costa suka halarta, gwamnatin Najeriya ta ba da fifiko wajen magance matsalar rashin tsaro a Najeriya, kungiyar ECOWAS, da yankin Sahel.

- Advertisement -

Ya kara da cewa hakan ba zai yi nasara ba idan ba tare da kasashen yankin da ma duniya baki daya ba.

“Ana magance ta’addancin Boko Haram a yankin Arewa-maso-gabashin Najeriya ta hanyar kokarin gwamnati, da kuma rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa (MJTF) na kasashe mambobin kungiyar,” inji shi.

Buhari ya bayyana fatansa na cewa ziyarar tasa za ta kara karfafa kyakkyawar niyya da hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu.

- Advertisement -

Ya kara da cewa, kafa kwamitin hadin gwiwa, wanda daya ne daga cikin muhimman batutuwan ziyarar, zai kara sa kaimi ga cimma burin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Ya kara da cewa, hakan zai sa a samu ci gaba, musamman ayyuka da tsare-tsare masu inganci don amfanin al’ummar kasashen biyu.

‘’A yau kasar Portugal tana shigo da kusan kashi 60 na iskar gas daga Najeriya wanda ya sa ta zama kasuwa ta biyu mafi girma a Turai.

- Advertisement -

‘’ Har yanzu akwai sauran abin da za a iya cimma a tsakanin kasashen biyu, musamman a yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine wanda ya kawo cikas ga ci gaba da samar da iskar gas zuwa Turai.

“Bugu da kari kuma, Najeriya na son ganin an raba kasuwanci zuwa kayayyakin da ba na mai ba kamar noma, ayyukan samar da wutar lantarki, makamashin da ake iya sabuntawa da kuma magunguna inda za a iya cimma nasarori masu yawa,” inji shi.

Shugaban ya jaddada bukatar sake farfado da yarjejeniyar samar da jiragen sama (BASA) da kuma kammala duk wasu yarjejeniyoyin da ake da su a kasashen biyu, ta yadda za a bunkasa harkokin tattalin arziki da zirga-zirgar jama’a a tsakanin kasashen biyu.

- Advertisement -

Ya kuma bayyana Najeriya a matsayin daya daga cikin kasashen da suka fi jan hankalin masu zuba jari a nahiyar Afirka, inda ya kara da cewa gwamnatinsa na ba da fifiko wajen gina muhallin kasuwanci.

‘’Najeriya na daga cikin yankin ciniki cikin ‘yanci na nahiyar Afrika (AFCFTA) – yanki mafi girma na ciniki cikin ‘yanci a duniya.

“Tare da yawan al’umma sama da miliyan 200 musamman matasa maza da mata, Najeriya kasa ce ta dabi’a kuma tana da kyau wajen zuba jari a kasashen waje da kuma samun kasuwa guda daya zuwa sama da kasashe 50,” in ji shi.

- Advertisement -

Dimokuradiyya ta rawaito, Shugaban na Najeriya ya yi marhabin da taron kasuwanci da aka shirya a yayin ziyarar da kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da dama tsakanin hukumomin bunkasa zuba jari na kasashen biyu da kuma cibiyoyin kasuwanci.

Ya bayyana rattaba hannu kan yarjejeniyoyin ”a matsayin kyakkyawan ginshiki na bunkasa kasuwancin kasashen biyu”.

Buhari ya kuma yabawa takwaransa na kasar Portugal bisa yadda kasarsa ta kara cudanya da nahiyar Afirka da kuma al’amuran Afirka fiye da kasashen Lusophone.

- Advertisement -

‘’A wannan yanayin, ina so in tunatar da mu cewa, baya ga ba da sunan tsohon babban birninmu, Legas, Turawan Portugal su ne Turawa na farko da suka fara zuwa kasar da ta zama Najeriya, tun kafin Turawan mulkin mallaka.

‘’A wancan lokacin, Masarautar Benin ta yi huldar diflomasiyya da Masarautar Portugal. An aika da masu gadin Oba na Benin daga Portugal.

‘’A yau, akwai tituna a wasu jihohi a Najeriya da har yanzu suna dauke da sunayen Portuguese. Wannan yana nuna kyakyawan alaka da ta dau tsawon lokaci a tsakanin kasashenmu biyu,’’ inji shi. (NAN)

- Advertisement -

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy