Tsoho Dan Shekara 80 ya Lashe Zaben Fidda Gwani A Jam’iyyar SDP

0

Tsoho Dan Shekara 80 ya Lashe Zaben Fidda Gwani A Jam’iyyar SDP - Dimokuradiyya

Wani tsoho dan shekara 80 Chief Bodunde Daramola yayi nasarar lashe zaben fidda gwanin dan takarar majalisar wakilai ta tarayya wato Oye dake jihar Ekiti karkashin jam’iyyar SDP.

Duk da cewa an yi yada jita jitar cewa jam’iyyar ta zabi sunayen wadanda taga dama ne, amma shugaban jam’iyyar Dele Ekunola ya Musanta zargin.

Ekunola ya ce wannan batu da ake yaɗawa ba gaskiya bane, domin kuwa sunayen da suka mika ga hukumar zabe mai zaman kanta INEC sunaye da aka zaba domin zama yan takarar jam’iyyar a zabe mai zuwa.


Download Mp3

Baya ga tsohon akwai tarin wasu mutanan da suka yi nasarar lashe zaben a jihar ta Ekiti karkashin jam’iyyar ta SDP, ciki kuwa har da sanatoci.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da matasa ke ci gaba da kokawa kan yadda masu shekaru suke danne madafun iko, duk kuwa da cewa basa iya taɓuka wani abun azo a gani.

Yanzu haka dai jam’iyyun siyasa a Najeriya na ta gudanar da zaben fidda gwanayen yan takarar su, gabanin babban zaben 2023.

Bayan da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta dage lokacin dakatar da zaben fidda gwanin bayan jam’iyyun sun bukaci a kara musu lokaci domin kammala zaben fidda gwanin.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy