Tsohuwar jaruma Fati Ladan da Yerima Shettima sun samu ƙaruwa

0

Tsohuwar jaruma Fati Ladan da Yerima Shettima sun samu ƙaruwa

Fati Ladan da Yerima Shettima tare da ɗan da Allah ya ba su a yau

A SAFIYAR yau Litinin, 11 ga Afrilu, 2022, Allah ya azurta tsohuwar jarumar Kannywood, Hajiya Fati Ladan, da santalelen ɗa namiji.

Fati ta haihu da misalin ƙarfe 8:17 na safe a wani asibitin kuɗi da ke Unguwar Rimi, Kaduna.

Idan masu karatu ba su manta ba, Fati Ladan ta kai tsawon shekara huɗu da aure kafin ta samu haihuwa, inda ta haifi ɗa namiji, amma kafin a yi suna Allah ya karɓi abin sa.

Sai kuma a ranar Talata, 21 ga Mayu, 2019 Allah ya azurta ta da santaleliyar yarinya, wadda aka raɗa wa suna A’isha, amma ana kiran ta Humaira. A yanzu haka saura kimanin wata ɗaya da kwanaki Humaira ta cika shekara uku a duniya.

Wani abin mamaki, an haifi Humaira cikin watan Ramadana, ga shi kuma wannan karon ma Fati ta sake haihuwa a watan Ramadana.

Allah ya raya, ya kuma albarkaci rayuwar sa, amin.

Fati Ladan dai ta na auren fitaccen ɗan gwagwarmayar nan kuma shugaban Ƙungiyar Tuntuɓa ta Matasan Arewa (Arewa Youth Consultative Forum), Alhaji Yerima Shettima.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy