Tsohuwar jarumar Kannywood Naja’atu Muhammad da ɗan ƙwallo Abdullahi Shehu sun samu ƙaruwa
Dakta Sarari (a hagu) tare da Missis Peace Anyiam-Osigwe da sauran shugabannin ƙungiyar jim kaɗan bayan zaɓen
A RANAR Laraba, 23 ga Maris, 2022 Allah ya albarkaci tsohuwar fitacciyar jarumar finafinan Hausa Naja’atu Muhammad, wadda aka fi sani da Murjanatu ‘Yarbaba, da mijin ta, wato fitaccen ɗan ƙwallon Nijeriya ɗin nan Abdullahi Shehu, da santalelen ɗa namiji.
Naja’atu ta haihu a wani asibiti a Istanbul, babban birnin ƙasar Turkiyya. Da ranar ta zagayo, jiya Laraba, aka raɗa wa yaro suna Abdulhameed.
Kasancewar ba a Nijeriya aka yi haihuwar ba, ba a yi wani shagali ba.
Naja’atu rungume da Abdulhameed
Abdullahi Shehu, wanda ɗan shekara 29 ne, Basakkwace ne. Ya na buga wa kulob ɗin Omonia na ƙasar Cyprus ƙwallo daga shekarar 2020.
Idan masu karatun mujallar Fim ba su manta ba, a ranar Juma’a ne, 18 ga Yuni, 2021 aka ɗaura auren sa da Naja’atu bayan an idar da sallar Juma’a a masallacin Juma’a na Umar Bin Khattab da ke Titin Zariya, Kano, a kan sadaki N50,000.
Allah ya raya Abdulhameed, ya kuma albarkaci rayuwar sa, amin.
Abdulhameed Abdullahi Shehu
