Ummi Rahab Tayi wuf! da Lilin Baba, har an biya sadaki an sa rana An Daura Aure

0

Ummi Rahab za ta yi wuf! da Lilin Baba, har an biya sadaki an sa rana

Amarya da ango, Lilin Baba da Ummi Rahab

FITACCEN mawaƙi kuma jarumi a Kannywood, Shu’aibu Ahmed Abbas, wanda aka fi sani da Lilin Baba, ya biya sadakin fitacciyar jaruma Ummi Rahab, kuma har an sa masu rana.
Tabbacin hakan ya fito ne daga Sulaiman Sir Zeesu, ɗaya daga cikin aminan Lilin Baba, a wani saƙo da ya wallafa a Instagram a daren jiya.

A saƙon, Sir Zeesu ya ƙara da cewa har an saka ranar bikin auren jarumar ta shirin ‘Wuff!’ da shi furodusa kuma jarumin shirin, tare da taya su murna.

Sai dai bai bayyana ranar bikin ba.

Ga abin da Sir Zeesu ya wallafa a shafin sa na Instagram:

Mun biya sadaki kuma an saka rana. Alhamdu lillahi ya Allah. It’s official. #SHURAN2022 Congratulations @lilin.baba @ummirahabofficial

Ɗan shekara 30 da haihuwa, shi dai Lilin Baba ɗan asalin Gwoza ne a Jihar Borno.

Ya shigo industiri a cikin 2016 a matsayin mawaƙi, inda ya fitar da waƙa mai taken ‘Arewa’.

Abin ya zo! Za su yi wuf! da juna

Kafin zuwan sa Kannywood, ya fara da tallar ƙanƙara ne (ice blocks) a bakin Bata, Kano, daga baya ya koma Abuja ya shiga sana’ar saida motoci.

Daga Abujan ne ya dawo Kaduna ya shiga harkar waƙa, kuma Allah ya yi masa nasibi a ciki.

A yanzu Lilin Baba ya na ɗaya daga cikin manyan mawaƙan Arewa, domin shi ne ma ya lashe gasar ‘Arewa Best R&B Music Act of the Year’ a bikin ‘City People Entertainment Awards’ na shekarar 2019.

Ya fara fitowa a fim ne a shirin ‘Hauwa Kulu’, yanzu kuma shi ne jarumin shirin nan mai dogon zango mai suna ‘Wuff!’ wanda ake nunawa a YouTube.

Labarin haɗewar sa da Ummi Rahab ba sabo ba ne, musamman bayan ya ƙwace ta daga hannun mawaƙi kuma jarumi Adam A. Zango, wanda ubangidan sa ne a da.

A lokacin rigimar jarumar da Zango, shi Zango ya zargi cewa wasu ne ke zuga ta har ta ke yo masa tsiwa, wanda a Kannywood an san da su Lilin Baba ya ke.

Ba da jimawa ba Lilin Baba da Ummi su ka bayyana soyayyar da ke tsakanin su da kuma niyyar su ta yin aure.

Yanzu ga abin zai tabbata. To, Allah ya sa alheri.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy