Wani Dan Takarar Gwamnan Jihar Abia A Jam’iyyar APC Ya Bukaci A Sake Sabon Zaben Fidda Gwani

0

Wani Dan Takarar Gwamnan Jihar Abia A Jam’iyyar APC Ya Bukaci A Sake Sabon Zaben Fidda Gwani - Dimokuradiyya

Wani dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Abia, Daniel Eke, ya bukaci a soke zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar a ranar 22 ga watan Mayu a jihar.

Emenike da tsohon minista, Uche Ogar, sun fito ne a matsayin ‘yan takara a zaben fidda gwani da aka gudanar a jihar.

Dan takarar wanda magoya bayansa suka gudanar da zanga-zangar lumana a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja, ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar APC na kasa da su shirya wani sabon zaben fidda gwani, kai tsaye da kuma sahihin zabe, inda za a bai wa duk masu son tsayawa takara daidai wa daida.


Download Mp3

Eke, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar Daniel Eke Support Group, Agbaeze Uche Okocha, ya fitar, ya shawarci jam’iyyar da ta kaucewa rugujewar doka da ka iya kawo mata cikas a babban zabe.

Ya kara da cewa abin da ya faru a ranar zaben fidda gwanin shi ne, babu daya daga cikin masu da’awar da ya cika ka’idojin da dokar ta tanada a matsayin dan takarar jam’iyyar, ya kara da cewa hanyoyin biyu ba za su iya cin jarabawar wadannan dokokin ba.

Ya ce, “Kwamitin zaben da ya zo Abia daga hedikwatar jam’iyyar ya gudanar da zaben fidda gwani na kai tsaye ba tare da sanar da Cif Daniel Eke lokaci, wurin da kuma yadda za a gudanar da zaben ba, duk da cewa ya sayi fom din nuna sha’awa da tsayawa takara a APC tare da sayen fom akan kudi har naira miliyan 50 kuma jam’iyyar ta tantance shi.

“Ya kamata kwamitin NWC ya shiga tsakani a yanzu sannan ta sanya sabuwar ranar zaben fidda gwani, sannan ta sanar da ranar ga duk masu son tsayawa takara, sannan ta ba da damar gudanar da zabe na gaskiya da adalci inda duk katin da ‘ya’yan jam’iyyar za su kada kuri’a a cikin tsari na gaskiya.”

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy