Wani ma’aikacin gwamnati ya maka Jaruma Hadiza Gabon a Kotu sabida taƙi aurensa bayan ta lakume masa kuɗi

0

Wani ma'aikacin gwamnati ya maka Jaruma Hadiza Gabon a Kotu sabida taƙi aurensa bayan ta lakume masa kuɗi

Wani ma’aikaci ya kai karar jaruma Hadiza Gabon gaban Kotun Shari’ar Musulunci kan ta karya masa alƙawarin aure.

Bala Musa ya shaida wa Kotun sun jima suna soyayya da Gabon kuma ta masa alƙawarin aure, shiyasa da ta nemi Kuɗi yake tura mata.

Lauyan da ke kare Gabon ya roki Kotu ta bashi isasshen lokaci domin ya zo da wacce yake karewa.

Kaduna – Wani mutumi ɗan shekara 48 ma’aikacin gwamnati, Bala Musa, ya maka Jarumar Kannywood, Hadiza Gabon a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kaduna ranar Litinin.

Daily Trust ta rahoto cewa Mutumin ya kai ƙarar jarumar ne saboda ta ƙi aurensa duk da kuɗaɗen da ya kashe a kanta.

Bala Musa ya shaida wa Kotun cewa sun jima suna murza soyayya da Jarumar kuma ta masa alƙawarin zata aure shi.

Ya faɗa wa Kotun cewa:

“Daga lokacin da muka fara soyayya zuwa yanzun na kashe mata kuɗi N396,000. Duk lokacin da ta nemi kuɗi ina bata ba tare da damuwa ba ina fatan wataran zamu yi aure.”

“Ta gaza zuwa Gusau, babban birnin jihar Zamfara inda nake zaune bayan na kammala duk wasu shirye-shiryen tarbarta.”

Hukumar Dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta ruwaito cewa a ranar 23 ga watan Mayu aka fara sauraron ƙarar, amma Hadiza Gabon ba ta samu halarta ba.

Shin Jarumar ta amsa laifinta?

Lauyan Hadiza, Mubarak Kabir, ya shaida wa Kotun cewa wacce yake kare wa ta gaza tabbatar da gaskiyar sammacin Kotu da aka kai mata.

Lauyan ya faɗa wa Kotu cewa:

“Wacce nake karewa ba fitacciyar mace ce da ke mu’amala da mutane daban-daban da niyya daban-daban. Ta na matuƙar kula da lafiyarta da tsaron kanta.”

Bayan haka Ƙabir ya roki Kotun ta ba shi lokaci isasshe domin ya gabatar da wacce yake karewa a gaban Kotu.

Alƙalin Kotun mai shari’a Malam Rilwanu Kyaudai, ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 13 ga watan Yuni, 2022.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy