Wasu Daga cikin Gwamnonin APC Sun Fara Karkata Ga Osibanjo, Gabanin Zaben Fidda Gwani

0

Wasu Daga cikin Gwamnonin APC Sun Fara Karkata Ga Osibanjo, Gabanin Zaben Fidda Gwani - Dimokuradiyya

Kwanaki kadan bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyanar da inda ya karkara ga wanda yake fatan ya gaje shi a zabukan fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC mai zuwa.

Yanzu haka da dama cikin gwamnonin jam’iyya mai mulki sun fara haduwa da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo wanda ake ganin ya dace da bayanin shugaban kasa

Gwamnonin jam’iyyar APC da dama ne aka hange su a fadar shugaban kasa a Villa inda suka gana da Osinbajo da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

Wannan dai wasu na ganin cewa lamari ne dake kasancewa wani yunkuri na samun amincewar dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar.

Rahotanni sun ce gwamnonin da aka gani a fadar Villa tsakanin Laraba zuwa yau Juma’a sun hada da na Kano da Ogun da Ekiti da Gombe da Nasarawa da kuma Ebonyi.

Rahotannin sun ce da alama akasarin gwamnoni 22 da ke karkashin jam’iyya mai mulki a karkashin kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC sun amince da goyon bayan takarar Osinbajo.

Hakan na zuwa ne gabanin zaben fidda gwani da za a fara ranar Litinin 6 ga watan Yuni bayan da aka dage gudanar da zaben a kwanakin baya.

Rahotanni sun bayyana cewa an samu karin gwamnonin Arewa da suka hada da na Borno da Kaduna da Kano da Nasarawa da kuma Gombe suna adawa da dan takarar shugaban kasa ya fito daga yankin Arewa a karkashin jam’iyyar APC.

Gwamnonin sun gudanar da tarurruka da dama a masaukin Gwamnan Jihar Kebbi da ke Asokoro, Abuja, a ranar Talata, bayan sun gana da shugaban kasa.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy