- Advertisement -

Wata Tirela Ta Murkushe Mutane 8, Raguna Sallah A Jihar Kwara

0

Wata Tirela Ta Murkushe Mutane 8, Raguna Sallah A Jihar Kwara - Dimokuradiyya

Rahotanni sun bayyana cewa a kalla mutane takwas ne da wasu shanu da ba a tantance adadinsu ba suka hallaka bayan wata motar tirela ta kasuwanci da ta taho daga yankin arewacin kasar ta kutsa cikin wata motar da ke tsaye a jihar Kwara.

- Advertisement -

An tattaro cewa lamarin ya faru ne a mahadar Okoolowo da ke karamar hukumar Ilorin ta kudu da misalin karfe 6 na safiyar Laraba.

A cewar wani mazaunin unguwar mai suna Salaudeen Abiola, direban tirelar da ke cike da shanu mai lamba DAT SGM396ZR ya kutsa kai cikin wata tirelar da aka ajiye a kan titin.

Ya ce wani namijin da aka yi imanin cewa shi ne mamallakin dabbobin da ke tare da direban ya mutu nan take.

- Advertisement -

“Sauran wadanda abin ya shafa sun hada da masu sayar da raguna da ‘yan kasuwa a kusa da wurin a lokacin da lamarin ya faru. kallo wajen yana da ban tsoro,” in ji shi.

Wani ganau ya ce akwai Hausawa 10 da Yarabawa biyu daga cikin wadanda abin ya shafa, ya kara da cewa an ajiye gawarwakin a dakin ajiye gawa na babban asibitin garin Ilorin.

Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta tarayya a jihar Kwara, Frederick Ogidan, ya tabbatar wa da manema labarai faruwar lamarin a ranar Asabar.

- Advertisement -

Ya ce, “Mutane 17 ne suka yi hatsarin, amma 8 daga cikin su sun mutu yayin da 4 suka jikkata.”

A wani labarin kuma Gwamnatin Tarayya ta fitar da sunaye da hotunan Ƴan Ta’addan da suka tsere daga Yarin Kuje

Gwamnatin Tarayya ta fitar da sunayen ƴan ta’addan da suka tsere daga Gidan Yarin Kuje, a lokacin da Mayaƙan Ƙungiyar Ta’addanci ta ISWAP ta shiga wurin.

- Advertisement -

Daily Trust ta ruwaito yadda Ƴan Ta’addan suka kai hari a gidan yarin Kuje dake Babban Birnin Tarayya Abuja a daren ranar Talata.

Bashir Magashi, Ministan Tsaro, yace dukkanin ƴan ta’addan dake tsare, ƴan Ta’addan sun sake su.

A ranar Juma’a, Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Aƙidu na Ƙasa (NCoS) ta saki sunaye da hotunan wasu daga cikin wanda suka tsere.

- Advertisement -

Daga cikin ƴan ta’addan da aka saki hotunan su, da sunayen su, sun ƙunshi Abdulkareem Musa, da Abdulkareem Adamu, da Abubakar Abibu, sa Kuma Abubakar Yusuf.

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy