Yadda Ɗan Takarar Jam’iyyar APC ya Lashe Zaɓen Ekiti, bayan yayi raga-raga da sauran Ƴan Takarkari
Yadda Ɗan Takarar Jam’iyyar APC ya Lashe Zaɓen Ekiti, bayan yayi raga-raga da sauran Ƴan Takarkari
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta INEC ta ayyana Ɗan Takarar Jam’iyyar APC Biodun Oyebanji, a matsayin wanda ya lashe zaɓen Gwamnan Jahar Ekiti.
Baturen Zaɓen Farfesa Kayode Adebowale wanda shine Shugaban Jami’ar Ibadan ya sanar da sakamakon Zaɓen.
Adebowale yace “,A yayinda Oyebanji ya kasance ya samu ƙuri’u fiye da kowa, a saboda haka na ayyana shi a matsayin Zaɓaɓɓen Gwamnan Jahar Ekiti.
Jam’iyyar APC ta samu ƙuri’u dubu 187,057 inda ya kada Abokin takarar sa na SDP da ƙuri’u dubu 82,211, a yayinda Jam’iyyar PDP ta samu ƙuri’u 67,457, da kuma sauran Jam’iyyu da suka Fafata a zaɓen Gwamna na ranar Asabar.
Daga cikin ƙuri’u dubu 360,753 da aka kaɗa, gaba ɗaya Sahihan Ƙuri’u sun kasance dubu 351,865.
A yayin da wakilin Jam’iyyar SDP, Omoseeni Ajayi yaƙi sanya hannu akan takardun cikewa, wakilin ADP yace “maimakon ace muna Akwatunan Zaɓe, mu a Ekiti wuraren sayen Ƙuri’u ke garemu”.
Haka zalika a Ado-Ekiti, Babban Birnin Jahar, tuni mazauna garin suka fito kan tituna domin nuna murnar su akan samun nasarar da daddare.
A gidan Gwamnatin dake Oke Ayoba, Sauran Gwamnonin APC ƙarƙashin Jagorancin Dr. Kayode Fayemi tuni sun shaida yanda aka gudanar da Zaɓen.
