Yan DR Congo Na Zanga Zanga Kan Zargin Da Suke wa Rwanda Na Goyon Bayan M23
Daruruwan al’umar a Kasar DR Congo sun Fito kan tituna sun yi dafifi tare da yin Tattakin a Birnin Kinshasa Babban Birnin kasar domin nuna adawar su ga Rwanda da suke zargi ta na goyon bayan Yan tawayen M23
Gamayyar kungiyoyin Fararan hula na kasar ne wato N-D-S-C-I suka shirya gangamin zanga-zangar.
A Ranar Litinin Shugaban kungiyar Tarayyar Afrika Kuma Shugaban Kasar Senegal Macky Sall a ya zanta ta Wayar tarho tare da takwarorinsu na Rwanda da Congo domin lalubo hanyoyin da za’a warware rashin fahimtar juna tsakanin Gwamnati in na Kigali da Kinshasa.
Sai dai tunda fari dukkannin kasashen na zargin junansu da tallafawa kungiyoyin tawaye dake Gabashin Jamhoriyar Dimokuradiyyar Congo.
Mr Sallah Wanda ya nuna damuwarsa kan rikicin kasashen biyu, ya bukacesu da su rungumi Shirin tattaunawa domin samun maslaha.
