Yan kungiyar Asiri 4 Sun Mutu, Yayin Raba Kudin Da Yan Siyasa Suka Basu A Bayelsa

0

Yan kungiyar Asiri 4 Sun Mutu, Yayin Raba Kudin Da Yan Siyasa Suka Basu A Bayelsa - Dimokuradiyya

Kimanin mutane hudu ne rahotanni suka ce sun rasa rayukansu a Swali na Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa, yayin da wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne suka yi artabu kan rabon kudaden da ‘yan siyasa daga yankin suka bayar.

Wannan na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan da al’ummar Yenagoa suka sanya dokar hana ayyukan asiri a yankin.

A cewar wata majiyar al’umma, wadanda aka kashe ana zargin ‘yan kungiyoyin asiri biyu ne da ake kira ‘Dey-riji da Bobos’.

Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa yayin da aka kashe mutane uku a unguwar Swali, an harbe daya da safiyar Lahadi a kan hanyar Osiri, unguwar Ekeki na Yenagoa.


Download Mp3

Rikicin baya-bayan nan na kungiyar asiri a birnin Yenagoa ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna birnin, wadanda galibin lokuta suke zama a gida don gudun kada a yi musu fashi.

Mazauna yankin sun yi kira ga gwamnatin jihar Bayelsa da ta dauki lamarin tsaro da muhimmanci tare da dakile tashe-tashen hankula a jihar.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Asinim Butswat, ya ce jami’ansu sun kama wasu mutane hudu da ake zargi da hannu a rikicin kungiyar.

Sai dai ya ce ‘yan kungiyar asiri biyu ne suka mutu a yayin rikicin.

Ya ce, “Mun kama mutane hudu da ake zargi da hannu a rikicin kungiyar, yayin da wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne suka mutu a rikicin. Ana ci gaba da bincike.” inji shi.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy