Yan Sandan Imo sun kama wata matashiya bisa zargin bautar da kananan yara

0

Yan Sandan Imo sun kama wata matashiya bisa zargin bautar da kananan yara - Dimokuradiyya

Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta tabbatar da cafke wata mata mai suna Victoria Nwosu ‘yar shekaru 26 da haihuwa, bisa zargin cin zarafi da kuma bautar da wasu ‘ya’ya guda uku.

Wani faifan bidiyo wanda ya bazu a yanar gizo inda aka ga kananan yara uku an daure su da sarka aka yi musu azaba ta ka da ta jiki.

Wani mazaunin yankin da abin ya faru, wanda ya yi faifan bidiyon, ya yi kira ga kungiyoyi da su kawo agajin yaran.

Daga bisani, kungiyar lauyoyin mata ta kasa da kasa reshen jihar ta shiga shirin daukar wani mataki, lamarin da ya kai ga cafke matar da mijinta.

Da yake tabbatar da kama matar, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Micheal Abattam, ya ce an kubutar da yaran ne kuma tawagar likitoci ta kai musu dauki.

Ya bada tabbacin za a gurfanar da ma’auratan a kotu a karshen binciken.

”A kokarin ceto yaran ne jami’an ‘yan sandan suka garzaya da su asibitin gwamnati da ke kusa da su inda aka yi musu magani aka sallame su.

Sai dai daga baya an mika su ga gidan marayun da gwamnati ta amince da shi, inda za a kula da su har zuwa lokacin da za a gano mahaifiyarsu.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy