Yan Sandan Zamfara sun kwato bindiga AK47, Da Harsashi 47, yayin Artabu da yan bindiga

0

Yan Sandan Zamfara sun kwato bindiga AK47, Da Harsashi 47, yayin Artabu da yan bindiga - Dimokuradiyya

Rundunar yan sandan jihar Zamfara tayi Nasarar kwari bindiga kirar AK47 guda daya daga hannun wasu yan bindigar, yayin da guda cikin su ya rabauta da harsashi da dama a jikinsa, wanda hakan ya sanya sai mushen sa.

Lamarin dai ya faru ne bayan da rundunar ta samu kiran gaggawa daga kauyukan Saran Gamawa, da kuma Unguwar Mata, cewa yan bindiga sun mamaye garin nasu.

Wata Sanarwa da mai magana da yawun rundunar SP Muhammad Shehu, ya aikowa da jaridar Dimokuraɗiyya ta bayyana cewa jim kadan da sumun kiran ne sai jami’an su na shirin ko ta kwana suka yiwa ƙauyukan kawanya.


Download Mp3

SP Shehu yace jami’an su hadin gwiwa da sauran jami’an tsaron sun samu nasarar fatattakar yan bindigar, wadanda da dama cikin su suka arce da Harbin bindiga a jikinsu.

Yayin arangamar dai yan sandan sun samu nasarar kwace harsashi 47, da sauran makamai daga hannun yan bindigar, wadanda suka watsar tare da neman tsira da rayukan su.

Tuni dai Kwamishinan yan sandan jihar Ayuba Elkanah ya bayar da umarnin bin sahun barayin, zuwa cikin dajin da suka bazama.

Daga nan sai kwamishinan ya bayar da tabbacin ci gaba da hada kai da sauran jami’an tsaro, domin tabbatar da tsaron rayuka da duniyoyin al’ummar jihar.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy