Yanzu Sai Damuwar Ta Koma Kanka — Tinubu Ya Yiwa Lawan Shaguɓe

0

Yanzu sai damuwar ta koma kanka — Tinubu ya yiwa Lawan Shaguɓe - Dimokuradiyya

Yanzu sai damuwar ta koma kanka — Tinubu ya yiwa Lawan Shaguɓe

Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC Ahmed Bola Tinubu ya yi wani jawabi ga Shugaban Majalisar Dattijai ta Ƙasa cewa yanzu sai dai damuwa ta koma kanshi.

Tinubu ya bayyana haka a ranar Laraba a lokacin da yake jawabin karbar ragamar mulki a filin wasa na Eagle Square, Abuja, bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe Zaɓen Fidda Gwani na Shugaban Ƙasa.

Tsohon Gwamnan Jahar Lagos yace bai ji daɗi yadda Lawan yayi takara dashi ba a neman tikitin Jam’iyyar, yana mai yi mashi Shaguɓe daya faɗi.

“Ga Ɗan Majalisa, Shugaban Majalisar Dattijai Ahmed Lawan, naji babu daɗi kaɗan domin kayi takara dani. Amma yanzu an gama sai kaje kayi ta fama da fushin ka.

Ya kuma godema Lawan akan irin ƙoƙarin sa na ciyar da Najeriya a gaba ta fuskar Majalisa.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy