Yanzu-Yanzu: Ken Nnamani ya fice daga takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC

0

Yanzu-Yanzu: Ken Nnamani ya fice daga takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC - Dimokuradiyya

Wani tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani, ya janye daga takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Nnamani ya bayyana janyewar sa ne a wata ganawa da ya yi da manema labarai a Abuja ranar Litinin.

Tsohon dan majalisar ya ce: “A halin da ake ciki yanzu babu wata ma’ana a gare ni in ci gaba da takara domin ban samu damar tallata bayanana da ra’ayoyina ga wakilan jam’iyyarmu ta hanyar da za a iya yin shawarwari ba.


Download Mp3

“Saboda haka, na dakatar da burina, ina yi wa jam’iyyar fatan samun nasarar gudanar da zaben fidda gwani da hadin kai domin mu samu nasara a babban zaben 2023.

“Zan ci gaba da yin cudanya da jam’iyyar da shugabanninta domin ganin cewa tunani da dabi’un da nake ji da su da yadawa sun samu gindin zama a cikin harkokin mulkin jam’iyya da shugabancin jama’a bayan zabe.”

A halin yanzu, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ta fara zaben fidda gwani na shugaban kasa a Abuja babban birnin kasar

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy