- Advertisement -

Yanzu Yanzu:- Matar Alaafin ta rasu makonni bayan rasuwar sarkin

0

Da-Dumi-Dumi: Matar Alaafin ta rasu makonni bayan rasuwar sarkin - Dimokuradiyya

Makonni kadan bayan rasuwar Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, daya daga cikin matansa, Olori Kafayat, ita ma ta rasu.

- Advertisement -

Majiyar jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa Olori Kafayat, wacce ita ce mahaifiyar Yarima Adebayo Adeyemi, wanda aka fi sani da D’Guv, ta rasu ne a daren jiya Juma’a.

Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba a kayyade cikakken bayanin rasuwar tata, amma Daraktan yada labarai na fadar Alaafin, Mista Bode Durojaye, ya tabbatar wa wakilin jaridar The Punch rasuwar tata a safiyar ranar Asabar.

Ya ce, “Ta rasu ne a kasar Amurka. Zan ba ku cikakken bayani a nan gaba.”

- Advertisement -

Idan ba’a manta ba, Oba Adeyemi ya rasu ne a ranar Juma’a 22 ga watan Afrilu a asibitin koyarwa na jami’ar Afe Babalola, Ado Ekiti, bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya yana da shekaru 83.

Har yanzu ba’a dana wani Alaafin na Oyo ba, tun bayan rasuwar Oba Adeyemi.

A wani labarin kuma na daban.

- Advertisement -

Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta bayyana cewa tana neman Olalekan Ajagungbade wanda aka fi sani da Emir da kuma wani mai suna Bode Olakayode wanda aka fi sani da Bode Itapa ruwa a jallo.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola ya rabawa manema labarai na wanda Jaridar Dimokuradiyya ta samu ta bayyana cewa an gurfanar da mutanen biyu bisa laifukan da ake zarginsu da su na kisan kai, kungiyar asiri, fashi da makami da kuma hada baki.

Sanarwar da rundunar ‘yan sandan ta fitar ta bayyana Olalekan Ajagungbade da cewa, “mai kimanin shekara 30 ne, yana da hasken fata, farare hakora, tsayin mita 1.75, hanci mai kauri, santsin kai, bakin gashi kuma dan kabilar Yarbawa ne.

- Advertisement -

“Wadanda ake zargin suna haddasa fitina a Osogbo da kuma jihar Osun baki daya.”

Ta kuma bayyana Bode Olakayode da cewa, ‘’dan kimanin shekara 34, bakar fata, fararen hakora, tsayin mita 1.70, hankici, bakin gashi kuma dan kabilar Yarbawa ne.

“Wadanda ake zargin suna haddasa rikici a Ilesa da kuma jihar Osun baki daya.”

- Advertisement -

Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta kuma yi gargadin cewa duk mutumin da aka kama yana tsare da wasu daga cikin wadanda ake nema ruwa a jallo, hukumar ‘yan sandan za ta dauki nauyin laifin da ake zarginsa da shi.

Yayin da yake kira ga ‘yan kasa da su tuntubi ofishin ‘yan sanda mafi kusa ta wadannan nambobi idan sun gansu kamar haka 08067788119, 08123823981, 08039537995 da 08075872433, rundunar ‘yan sandan Osun ta kuma bayar da tabbacin cewa duk wanda ya bayar da bayanai masu amfani dangane da inda suke za a ba shi ladan.

- Advertisement -
wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy