Yarabawa sun sake baiwa Ganduje sarauta, saboda riƙo da addinin sa

0

Yarabawa sun sake baiwa Ganduje sarauta, saboda riƙo da addinin sa - Dimokuradiyya

Majalisar Malamai ta jihohin Yarbawa ta baiwa gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje sarautar Alaudden of Yourubawa.

Wanan na zuwa ne kwanakin biyu bayan da Alafin na Oyo ya naɗa gwamnan da matarsa sarautar AARE Fiwajoye and YEYE AARE Fiwajoye na kasar Yarubawa.

Gwamnan ya sake samu Sabuwar sarautar a ranar Asabar 18 ga Yuni da muke ciki.


Download Mp3

Shugaban majalisar limamai da malamai na Jihar, Oyo Sheikh Abdulganiyyu Abubakar ne ya nada gwamnan a madadin limanan.

Da yake jawabin Sheikh Abdulganiyyu ya ce ana bayar da sarautar ne ga Musulmi mai riko da addini da kuma yi wa addinin hidima.

A cewarsu binciken su ya tabbatar musu Gwamna Ganduje ya cika wannan sharuddan.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy